JAWABIN SHEICK NA BANA A GARIN ABUJA

Submitted by ahmadmd on Mon, 04/16/2018 - 17:10
ALLAH YA BIYA DA GIDAN ALJANNAH JAWABIN SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI TA KASA DA KASA TA HADADDIYAR KUNGIYAR JIBWIS NATIONAL HEADQUARTERS JOS ASH-SHEIKH MUHAMMAD SANI YAHAYA JINGIR WANDA YAYI A RANAR BABBAN TARO NA SHEKARA-SHEKARA NA KASA (JIBWIS ANNUAL ISLAMIC CONVENTION ABUJA 1439/2018) A EAGLE SQUARE DAKE BABBAN BIRNIN TARAYYAR NIGERIA, F.C.T. ABUJA A RANAR LAHADI 15 GA RAJAB 1439 DAIDAI DA 1 GA AFRILU, 2018 ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻭﺇﻣﺎﻡ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ، ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﻣﻦ ﺗﺒﻌﻬﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﻭﺑﻌﺪ : ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺑﺮﻛﺎﺗﻪ : 1. Gabatarwa: Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki mai kowa mai komai, mai rahma mai jin kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, Allah yasa da mu cikinsu, amin. Bayan haka, wannan hadaddiyar kungiya ta JIBWIS wacce marigayi Ash-Sheikh Isma'ila Idris Allah ya kaddareshi da kafawa kamar shekaru talatin da tara da suka wuce, tana wa'azin Musulunci a Nijeriya da kasashen dake makwabtaka da ita a nahiyar Africa da sasannin Duniya akan dukkan fannonin rayuwar Musulmi bisa shari’ar Allah da sunnonin Manzon Allah (S.A.W). Wannan kungiya tana fifita karantar da tauhidi a matsayin tushen ibada a musulunci, ta hanyar tsarkake Allah (SWT) da kadaita shi a wajen bauta da barin dukkan nau'o'in shirka, Bidi’o’i, bokanci, camfe-camfe, tsafi, da kashe mutane ta hanyar amfani da kungiyoyin asiri, da sauran abubuwa da shari'ar musulunci ta bayyana na haramci. Har yanzu kungiyar tana wa'azi da karantarwa akan muhimmancin zaman lafiya, da'a ga shugabanni, tausayawa talakawa ta hanyar rike amanar shugabanci da raya ilimi da ilmantarwa don muhimmancisa ga cigaban rayuwar al'umma. Wadannan ayyuka na wa'azozi da ilmantarwa ana gudanar da su ne ta hanyoyin wa’azin kasa a cikin kasa da waje duk bayan mako uku, wa'azozin jihohi, kananan hukumomi da na rassa, tarukan karawa juna ilimi (Seminar), Gasar karatun Al-Qur'ani mai girma tun daga matakan kasa zuwa rassa, bude makarantu na yara, da manya maza da mata a matakai daban-daban, da tafsirin Al-Qur'ani mai girma a Nijeriya da kasashen waje, bude sashin ilmantar da Alkalai, Shugabanni, Limamai da Ladanai makamar ayyukansu daki-daki da buga littattafai da sauran hanyoyin da suka dace na yada ilimi da ilmantarwa, bayannan da zasu biyo da nasarorin da wannan kungiya ta samu zasu kara tabbatar da manufofinta da ayyukanta, da fatan Allah ya kara mana taimako akan wadannan ayyuka na alheri da ciyar da kasarmu gaba da sauran kasashe, Amin. 2. NASARORI: Sakamakon ayyukan kungiya da suka gabata da hanyoyin da ake aiwatar da su, kungiyar ta sami nasarori kamar haka: a) Kungiyar na samun nasarori masu dinbin yawa da karin hadin kai da son juna tun daga kafata har zuwa hadewar wannan kungiyar da Allah (SWT) ya nufeta tayi Ranar 26 Muharram 1433 dai-dai da 21st December 2011. Kungiyar ta samu nasarorin ilmantar da al’ummar Musulmi da makwaftansu wajen kawar da:- - Jahilci, - Shirka, - Bidi’o’i, - Ki-ki juna na kabilanci da sauran laifuka. Kuma wannan hadewa ta cimma babbar nasara na haduwar dukkan Ahlus-sunnah muna aiki babu wani ce-ce kuce. A nan nake kara yabawa mataimakana na daya da na biyu Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachukum da Sheikh Sa’id Hassan Jingir da Shugaban Gudanarwa da mataimakansa Sheikh Abdun-Nasir Abdulmuhyi, Alh. Hashimu mai Atamfa Kaduna da Dr. Sani Aliyu Sagir Sokoto da Shugaban Yan Agaji da mataimakinsa Alh. Isa Waziri Muhammad Gombe da Alh. Ibrahim Shu’aibu Ishaq da dukkan shugabanni a matakin Kasa, Jihohi, Kananan Hukumomi, Rassa da sauran ma’aikata da daidaikummu, Allah ya ka ra muku albarka, Ya sa ka muku da alheri. b) Mun sa mi nasarar gabatar da wa'azozi a mataki na kasa cikin Nijeriya har (10). 1438/2017. c) Mun yi nasarar tura malaman tafsiri a watan Ramadan wurare daban-daban a cikin kasa da kasas

SHEICK YAYI WA'AZI MAI ZAFI

Submitted by ahmadmd on Mon, 04/16/2018 - 17:02
SHEIKH SANI YAHYA JINGIR YAYI MARTANI GA WAKAR:- Afuwan-Afuwan Ya Barhama::- Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS na Kasa,Mai Head/Qrt's ajos. Ash-sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir Yagabatarda Gagarumin Wa'azi amasallacin Yan-taya agarin Jos aranan Juma'a data Gabata 13-4-2018, Dattijun Shehun .