ALFAHARI DA CERTIFICATE.

Submitted by danmaliki on Mon, 12/26/2016 - 21:21
ALFAHARI DA CERTIFICATE: Wata Magana ta Hikima da Shaikh Isma'ila Idris Bin Zakariyya.Rtd ya fada ga dalibai masu neman Ilimi yace: ﺍﻟﻌﻘﻴﺪﺓ ﺍﻟﺴﻠﻔﻴﺔ ﺍﻟﺼﺤﻴﺤﺔ ﺧﻴﺮﻣﻦ ﺷﻬﺎﺩﺓ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﺔ ''Akida ta salafiyya Ingantacciya tafi Alkhairi (gare ka) fiye da shaidar da zaka samu (a karatu)''. Kusan shekara 20+ da fadin wannan magana ta shi. Watakila saboda a lokacin ya lura da wasu dalibai ne 'kila sunfi fifita certificate na karatu fiye da Ingantacciyar A'kidar Ahlus sunnati Wal Jama'ah. Yanzu Alfahari da certificate akeyi harma ana dauka inba ka da certificate to karatunka na Banza ne, baza ayi da kai ba. Lallai wannan magana da Sheikh ya yi ba 'karamin Hannunka Mai Sanda ya yi ga 'Dalibai masu neman Ilimi ba. Lallai kayi 'ko'kari a fagen neman Ilimin ka ka fifita A'KIDAR KA fiye da wata shaida da za a baka na karatu, ko wata titles da za a baka, duk wannan shaida (certificate) ko Title da za a baka shirme ne kuma asara ne gare ka idan har basu zame ma ka hanyar shiga Aljanna ba. Kar ka rudi kanka da cewa ana kiranka da wata titles kamar Engr, SA, PA, His/Her Excellency, Doctor, Proffessor, Lecturer, His Royal Highness, Commander In chief. Dss. Duk wainnan shirme ne da hayaniya gare ka idan baka da Ingantacciyar A'kida ta musulunci. Saboda haka a takaice abinda Mallam yake nufi shine: Duk wanda zayyi karatu, to ya tsarkake niyyar sa ya zama don Allah zayyi da shahada ko ba shahada. Allah ya Jikan Mallam da Rahama, Mu kuma da muke raye Allah ya bamu Ilimi mai Albarka, Allah yasa mu samu Husnul Khaatima.

MURNAR MAULIDI KO QAGE??.

Submitted by danmaliki on Wed, 12/21/2016 - 20:07
MURNAR HAIHUWAR ANABI KO QAGE? {Ta bakin Ustaz Ibrahim Umar Jos} Duk mai shekaru kaman nawa ko sama danl ko kasa da nawa kadan yasan lokacin da ba'a maulidi. Da wayonmu aka fara maulidi kuma sau 1 tak akeyi a shekara tafiya tayi tafiya anayi sau 2 a shekara ran haihuwa da ranan suna. yanzu kowane mai hali sai yayi a kofar gidan sa. Yanzu kuwa sau nawa ake yi a wata???. An dawo harma tarayan wata sukeyi yanzu!. Na 1 inda Addini ne wa yabada umurni Afara sau 1 a shekara sannan a dawo sau 2 a shekara daga baya a dawo babu adadi? lokacin da aka fara maulidi karatun alqur'ani da alburda da ishiriniya akeyi in banda yabon Annabi (saw) ba'a yabon kowa yanzo haka ake yi?? A wancan zamani ba taron maza da mata yanzu kuwa mata sunfi maza yawa wurin maulidi. Annabi (saw) yace ku nesanta tsakanin numfashin maza da mata. Ina rokon Allah ya nuna mana gaskiya ya bamu ikon Binta ya nuna mana bata ya bamu ikon guje mata. Allah ya doramu a kan dai dai amin.