JADAWALIN KASAFIN KUDIN AIKIN HAJJIN BANA

Submitted by ahmadmd on Wed, 05/31/2017 - 11:19
Maniyyata aikin hajji daga Najeriya za su biya fiye da Naira 1,500,000 kafin su sami sauke farali a bana. Zuwa yanzu, hukumar kula da ayyukan Hajji ta Najeriya ta fitar da farashin da ko wanne maniyyaci daga jihohi 22 cikin 36 na kasar zai biya. Mafi kankantar farashin shi ne na Naira 1,480,000 da maniyyatan jihar Katsina za su biya. Maniyyatan jihar Oyo sune zasu biya farashi mafi yawa na Naira 1,584,069. Bashir Abubakar El-nafaty mazaunin Abuja kuma maniyyaci ne a bana ya koka da yadda aka sami karin farashin aikin hajjin na bana. "A gaskiya farashin nan da aka fitar bai yi mana dadi ba", in ji Bashir. "Wannan karin kudin ba kadan ba ne, kuma ya bata wa maniyyata lissafinsu." Mallam Bashir ya shafe shekara guda yana ajiyar kudaden aikin hajjin. "Kafin karin dai na ajiye naira miliyan daya, sai kwatsam muka ji an kara Naira 500,000. A da muna fatan karin da za mu yi ba shi da yawa", in ji shi. A bara dai maniyyata daga arewacin kasar sun biya Naira 998,248.92 a karamar kujera, wasu kuma sun biya Naira 1,047,498.92 na matsakaiciyar kujera, kana masu babbar kujera sun biya Naira 1,145,998.92. Su kuma maniyyata daga kudancin kasar sun biya Naira 1,008,197.42, su kuma masu matsaikaiciyyar kujera kuma sun biya N1,057,447.42, inda masu babbar kujera suka biya Naira 1,155,947.42. A bana an soke wannan tsarin kujeru daki-daki, inda aka mayar da shi na bai daya, kuma kowane maniyyaci zai biya abin da jiharsa ta kayyade. A bana an tsayar da guzurin bai daya na dala 800 na Amurka. An kara kudin kujerar Hajji a Kamaru Musulman Guinea sun kasa zuwa Hajji Nigeria

YADDAH LABARAI KE ISKE WANNAN SHAFI DANGANE DA YADDAH TAFSIRAI KE GUDANA A FADIN DUNIYA NA WANNAN QUNGIYA

Submitted by ahmadmd on Mon, 05/29/2017 - 14:26
YADDAH LABARAI KE ISKE WANNAN SHAFI DANGANE DA YADDAH TAFSIRAI KE GUDANA A FADIN DUNIYA NA WANNAN QUNGIYA UPDATE FROM MASALLACIN ROKON RUWA NA SHEIKH USMAN FODIYO SOKOTO JAWABIN BUDE TAFSIR KENAN DAGA BAKIN SHEIKH SAED HASSAN JINGIR UBAN MATASA MATAIMAKIN SHUGABAN MAJALISAR MALAMMAI NA KASA NA BIYU TARE DA JAWABIN SHEIKH ABUBAKAR USMAN MABERA SHUGABAN MAJALISAR MALAMMAI NA JAHAR SOKOTO ALHAMDULILLAH _______________ RAMADAN TAFSIRI ALLAH YANUFI ISOWAR SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI NA JAHAR KEBBI ASHEIKH ABDURRAHMAN ISAH JEGA ISOWA MASALLACIN JUMUA NA TSOHUWAR MAYANKA BIRNIN KEBBI DOMIN BUDA TAFISIN RAMADAN TAREDA ALHAFIZ NAZIRU ABDULLAHI JEGA MUNA ROKON ALLAH YAMA MALAM JAGORANCI