HADIN KAN AL-UMMAR MUSULMAI FARILLAHNE BA......….

Submitted by ahmadmd on Wed, 03/07/2018 - 14:29
Sambo Rigachukun Sheikh Yusufu To muna fatan Allah ya kara hada kammu akan gaskiya Domin ni dai dan gajeren zangon ilimina abinda yake sanar dani shine duk lokacinda kaga al,ummar musulmi cikin kaskanci da wulakanci To sun bar Allah ne ,Amma idan har musulmi suka bar Allah sukayi watsi da bin Sunnar manzon Allah suka koma basu da banbanci dasu da wadanda ba musulmiba wajan aikata kowani irin nau,in sabon Allah To wallahi su saurari zuwan Bal,i Ayoyi da dimbin hadisai duk sun tabbatar da haka To kuma Ni babban abinda yafi damuna shine malamai sun kasa yarda su hada kai waje daya kuma wallahi badan komai bane , sai don Son Duniya na neman shugabanci da son daukaka .Anyi watsi da abinda hadisi da tauhidi suka tabbatar mana na cewa kowa Allah ya riga ya rubuta mishi nau,in irin arzikinshi da abinda zai samu da abinda zai zama tun yana cikin cikin mahaifiyarshi 1 an rubuta arzikinshi 2 an rubuta ajalinshi 3dama irin nau,in aikinshi 4 haka kuma an riga an rubuta Shi dan wutane ko dan aljanna ne To idanko har da gaske mun fahimci haka to Menene abin fada ko rikici ko jayayya Kuma su malamai sunefa likitocin Duniya akan ko wace irin cuta da zata kama dan Adam To sai suma suka kamu da irin wannan cutar To yaya zasu iya gyara wani? Mutum ne yazo maka da maganin Mura yana Talla To amma kuma shima gashi yanata Atishawa kuma ruwan majinar mura yana zubowa daga hancinshi To yaya zaayi kasayi maganin tunda shima mai sayar da maganin bai warke ba Saboda haka Malamai kuji tsoron Allah ku hada kai domin kawunan mabiya ya hadu guri daya Domin duk matsalar daga wajenkune da zarar kun gyaru to Suma mabiya zasu gyaru wanda kuma yaki To mu sai mubar ai,amarinshi zuwa ga Allah shi Allah shi yasan abinda zai

MATSAYIN MAI KALLON FILM DIN TSIRAYCI SHI DA IYALINSA

Submitted by ahmadmd on Wed, 03/07/2018 - 09:41
Mene hukuncin magidancin da ya ke kallon film din dake nuna tsiraici da matarsa a musulunci? AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’una, lallai al’umar musulumi mun samu kanmu a halin koma baya da tabarbarewar dabi’u. Amma Annabi (SAW) yayi gaskiya, inda ya ce: lallai za ku bibiye halaye irin na mutanen da suka gabaceku. Baya hallata ga musulumi kallon fina-finan da ake nuna tsiraici, ko hutunan da ke baiyyana tsiraici, ko kallon tsiraicin a zahiri, mutum shi kadai ne ko tare da matarsa ta Sunnah. Al-kur’ani mai Girma yana cewa a cikin suratun-nur: ‘ Ka fadama muminai maza su rintse idanuwansu kuma su tsare farjinsu. Wannan shi ne yafi tsarki agaresu, kuma