RAHOTO KAN WA'AZIN KASA A GARIN ABUJA

Submitted by ahmadmd on Thu, 03/30/2017 - 20:10
Kungiyar Izala Ta Yi Taron Wa’azi Domin Raya Ilimi Da Sahihiyar Akidar Islama A Abuja Maris 28, 2017 Ibrahim Jarmai Rarraba See comments Kungiyar Izala, mai shelkwata a Jos, jihar Plateau, ta zage damtse wajan kammala cibiyar raya ilimi da sahihiyar akidar Islama, a babban birnin tarayya Abuja. WASHINGTON D.C — Wannan yunkuri na kungiyar nada nasaba da cusa akida mai kyau ga al’ummar musulmi, biyo bayan nasarar da gwamnatin Najeriya, ta cimma na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, da kuma nasarar da zata inganta wajan ci gaba da wa’azi, da kafa makarantu da kuma sauran cibiyoyin da zasu rika ilimantar da al’umma akan addinin musulunci da kuma ilimin zamani. Kungiyar ta gudanar da wani gagarumin wa’azi a birnin tarayya Abuja, domin karfafa wannana kuduri da kuma manufa kamar yadda shugaban majalisar malamai na kungiyar a Abuja, Ustaz Ibrahim Duguri, ya bayyana. Mai wa’azi na kungiyar sheik Bashir Kashere, ya karfafa ayyukan kungiyar na marawa neman ilimi baya. Kungiyar ta yi amfani da wannan dama wajan kira ga majalisun dattawan Najeriya, da su rika mayar da hankali wajan abubuwan da suka shafi kasa kamar yadda sheik Sani Yahaya Jingir, shugaban majalisar malaman kungiyar na kasa ya yi Karin bayani. Daga karshe kungiyar ta kaddamar da littafi mai taken Boko Halal, dake karfafawa mutane gwiwa wajan neman ilimi da cire tsoron ‘yan ta’adda dake hana al’umma sukunin neman abin tallafawa ta hanyoyin halal.

WA'AZIN KASA ABUJA

Submitted by ahmadmd on Sat, 03/25/2017 - 20:16
Mp3 Audio na wa'azin Abuja, kayi downloading ka saurara. JIBWIS ANNUAL ISLAMIC CONVENTION, ABUJA 2017: 1. Ustaz Ibrahim Duguri, http://kiwi6.com/file/hx8zn13ts2 2. Dr Hassan Dikko, http://kiwi6.com/file/f5e5kdt9s2 3. Sheikh Madu Mustafa

NASIHAR JUMA'A TA YAU 24/033017

Submitted by ahmadmd on Fri, 03/24/2017 - 13:33
Mashaa Allah. Yau juma,a 26/06/1438-24/03/2017 kuma itace jajiberen tafiya zuwa wa,azin na kasa don raya ilimi na qungiyar jibwis Nhq jos,karkashin jagorancin shugaban majalisar malamai ta kasa Assheikh Muhammad Sani Yahaya jingir a garin Abuja a Nigeriya,kamar yadda aka saba duk juma,a ga malam din yana karantar damu addini umarni da hani kamar yadda aka saukar musamman akan shan giya da caca da kuma bokanci,muna addua Allah yakaremu kamar yadda Allah yace ku nesanci dukkan sa6o ko kwa sami babban rabo.Muna fatan Allah yabamu ikon zuwa wannan wa,azi yakaimu lafiya yadawo damu lafiya. A karshe malam yayi addua Allah yakara mana zaman lafiya a wannan kasa tamu,Allah yabawa shugaban kasa nasara wajen jagorantarmu ya kara masa lafiya.

INNA'LILLAHIWA INNA'ILAIHIN RAJI'UN

Submitted by ahmadmd on Fri, 03/24/2017 - 12:10
INNALILLAHI WA INNAA ILAIHIR RAAJI'UN!!! ALLAH YA YIWA MAI MARTABA SARKIN DEBA RASUWA. Marigayi Mai martaba Sarkin Deba Lt Col. Abubakar Waziri Mahdi, Ya rasu a asibitin Turkish dake Abuja. Allah ya jikan sa da Rahma yasa Aljannah fiddaus ce makomarsa da mu baki daya. Muna kara mika ta'aziyar mu ga Masarautar Deba karamar hukumar Yamaltu Deba dake jihar Gombe.