BA'A DA'AWA DA RAGONTA RAGO BAZAI IYAH BAH

Submitted by ahmadmd on Fri, 12/29/2017 - 18:47
BA'A DA'AWA DA RAGONTA RAGO BAZAI IYAHBAH. Daga inakake karanrantarwa inazaka karantarwa Mashaa Allah Yau juma,a 10/04/1439-29/12/2017 kuma ta farko bayan dawowa daga wa,azin kasa a garin wase jihar plateau. Gamu a gaban Shugaban majalisar malamai ta kasa Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya jingir tareda Hafiz Abdurrahman Ahmad,suna karantar damu addini. Cikin karantarwar ta Malam ya fara da tauhidi kamar yadda yasaba,sannan Malam yakara karantar damu sanin muhimmancin bako idan yazo mana,har Malam yakawo tarihin Annabi Ibrahim (A.S) yadda yake karrama baki. Sannan kuma Malam yakawo hadisin Manzon Allah Annabi Muhammadu (S.A.W) akan karrama bako. Malam yakara karantar damu muji tsoron Allah kada mu sa6a masa domin musami tsira gobe kiyama. Malam yakara addua ga jama,ar kasa da duniyar musulmi baki daya,Allah yakara mana tsaro yakaremu daga dukkan sharri. Malam yayi addua ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da majalisarsa ta kasa da Gwamnoni da majalisunsu da shugabannin kananan hukumomi da majalisunsu,Allah yakara musu jagora kuma yakara musu hadinkai don su samu suyi mana aiki mu talakawa.