IZALAH SARKIN AIKI GAYYATA ¥ GAYYATA ¥

Submitted by ahmadmd on Tue, 01/30/2018 - 19:06

GAYYATA! GAYYATA!! GAYYATA!!! Kungiyar Izala Za Ta Bude Katafaren Ofishin Ta A Garin Jos Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, Shugaban Majalisar Malamai ta kasa da Ash-Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigacikum da Ash-Sheikh Saeedu Hassan Jingir, da Ash-Sheikh Nasir Abdulmuhyi Shugaban Majalisar gudanarwa ta kasa, da Shugaban Rundunar Agaji ta kasa Ustaz Isa Waziri Muhammad Gombe, Suna gayyatar al'ummar musulmi zuwa bude Babban ofishin kungiyar Jama'atu Izalatil Bid,ah Wa'ikamatis Sunnah ta kasa wacce take da shalkwata a cikin garin Jos. Wanda za a yi ranar Asabar 03/02/2018 da misalin karfe 10:00 am inshaa Allah. Wuri: Layin Sarkin Mangu Jos. Allah yabada ikon zuwa amin. Sanar daga Hamza Muhammad Sani, National Organising Secretary Internet Media Committee Jibwis Nhq Jos.

Comments