Difa'u

Submitted by admin on Mon, 10/10/2016 - 19:19

Comments

Permalink

ISTIQAMA (TSAYAWA AKAN ADDINI BA TARE DA GAJIYAWA KO JA-DA-BAYA BA). Idan aka bawa al'ummah tarbiyya, Ilmi, sana’a, da koyar dasu da'a, sai kuma a nuna musu mihimmanci kafuwa akan riko da addini sosai, babu rawar kafa, babu ja-da-baya. Mutane su zama suna rokon Allah akan istaqama Allah Ta’ala yana cewa: رَبَّنا لا تُزِغ قُلوبَنا بَعدَ إِذ هَدَيتَنا وَهَب لَنا مِن لَدُنكَ رَحمَةً ۚ إِنَّكَ أَنتَ الوَهّابُ Yã Ubangijinmu! Kada Ka karkatar da zukãtanmu bãyan har Kã shiryar da mu, kuma Ka bã mu rahama daga gunKa. Lalle ne, Kai, Kai ne Mai yawan kyauta. (Quran-3:8). TSAYUWA AKAN ADDINI (ISTIQAMA) NE ZAISA MATASA SU BAWA ADDINI GUDUMAWA SOSAI: Allah Yana cewa: 1. Hatta a lokacin rasuwa, mala'iku suna bushara ga masu imani da istiqama. إِنَّ الَّذينَ قالوا رَبُّنَا اللَّهُ ثُمَّ استَقاموا تَتَنَزَّلُ عَلَيهِمُ المَلائِكَةُ أَلّا تَخافوا وَلا تَحزَنوا وَأَبشِروا بِالجَنَّةِ الَّتي كُنتُم توعَدونَ Lalle waɗannan da suka ce: "Ubangjinmu, shĩ ne Allah," sa'an nan suka daidaitu, malã'iku na sassauka a kansu (a lõkacin saukar ajalinsu sunã ce musu) "Kada ku ji tsõro, kuma kada ku yi baƙin ciki, kuma ku yi bushãra da Aljanna, wadda kun kasance anã yi muku wa'adi da ita." (Fussilat Quran-41:30). 2. (Ibraheem Quran-14:27). Wannan ayar kuma tana magana akan tabbatuwa akan Tauhidi. يُثَبِّتُ اللَّهُ الَّذينَ آمَنوا بِالقَولِ الثّابِتِ فِي الحَياةِ الدُّنيا وَفِي الآخِرَةِ ۖ وَيُضِلُّ اللَّهُ الظّالِمينَ ۚ وَيَفعَلُ اللَّهُ ما يَشاءُ Allah Yanã tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni da magana tabbatacciya a cikin rãyuwar dũniya, da cikin Lãhira, Kuma Allah Yanã ɓatar da azzãlumai, kuma Allah Yanã aikata abin da Yake so. 3. ( Muhammad Quran-47:7) . Taimakawa addini yana jawo mutum ya zama mai Istiqama. يا أَيُّهَا الَّذينَ آمَنوا إِن تَنصُرُوا اللَّهَ يَنصُركُم وَيُثَبِّت أَقدامَكُم Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Idan kun taimaki Allah, zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugãduganku. 4. ( Hud Quran-11:120): karanta tarihin magabata da koyi dasu yana tabbatar da Istiqama. وَكُلًّا نَقُصُّ عَلَيكَ مِن أَنباءِ الرُّسُلِ ما نُثَبِّتُ بِهِ فُؤادَكَ ۚ وَجاءَكَ في هٰذِهِ الحَقُّ وَمَوعِظَةٌ وَذِكرىٰ لِلمُؤمِنينَ Kuma dũbi dai Munã bã da lãbãri a gare ka daga lãbarun Manzanni, abin da Muke tabbatar da zuciyarka da shi. Kuma gaskiya ta zo maka a cikin wannan da wa'azi da tunãtarwã ga mãsu ĩmãni. 5. (Furqan Quran-25:32) .karanta Al-Qur'ani da Tadabburin sa yana Sanya Istiqama. وَقالَ الَّذينَ كَفَروا لَولا نُزِّلَ عَلَيهِ القُرآنُ جُملَةً واحِدَةً ۚ كَذٰلِكَ لِنُثَبِّتَ بِهِ فُؤادَكَ ۖ وَرَتَّلناهُ تَرتيلًا Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ãni a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Dõmin Mu ƙarfafa zũciyarka game da shi, kuma Mun jẽranta karanta shi da hankali jẽrantawa. 6. Kuma Wanda yayi da'a, yayi Aiki da wa'azi zai samu istiqama. ولو أنهم فعلوا ما يوعظون به لكان خيرا لهم وأشد تثبيتا 7. (Anfal Quran-8:12) Hatta wajen jihadi ana tabbatar da masu imani. إِذ يوحي رَبُّكَ إِلَى المَلائِكَةِ أَنّي مَعَكُم فَثَبِّتُوا الَّذينَ آمَنوا ۚ سَأُلقي في قُلوبِ الَّذينَ كَفَرُوا الرُّعبَ فَاضرِبوا فَوقَ الأَعناقِ وَاضرِبوا مِنهُم كُلَّ بَنانٍ A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: "Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu. Annabi SAW yana cewa: عن سفيان بن عبد الله رضي الله عنه قال : قلت : يا رسول الله قل لي في الإسلام قولاً لا أسأل عنه أحداً غيرك , قال : قل آمنت بالله ثم استقم ” رواة مسلم , Don haka matasa Ku tsaya akan Aqeeda mai kyau, Ku zama masu tauhidin Allah wajen Ibada, kuma Ku kula da Tauhidul Mutaba'a (tauhidin Manzon Allah wajen Risala). Ku tsaya akan tafarkin magabata, kuyi ibada irin nasu, Ku tsaya akan abinda suka rubuta na Fiqhu, Hadith, Tafsir da sauran fannonin ilmi. Saboda haka mu tsaya akan addini ba rawan kafa, ba ja-da-baya. Allah Ta'ala muke roko Ya tabbatar damu