MUSABAKA TA JIHIR PLATEAU A GARIN WASE

Submitted by ahmadmd on Wed, 04/26/2017 - 09:55

MUSABAKA! MUSABAKA!! MUSABAKA!!!

مسابقة القرآن الكريم وتجويده وتفسيره. 

لجماعة إزالة البدعة وإقامة السنة

فرع ولاية بلاتو

----------------------------------------------

Sheikh, Dr. Hassan Abubakar Dikko - shugaban majalisar malamai na Jihar Pilato, da shugaban gudanarwa Alh. Dogara Ishaka Dogara, da Shugaban Rundunar sojojin sunnah na Jihar Ustaz Muhammad Rabiu Musa, tare da babban jami'in lura da shirya Gasar karatun Al-qur'ani mai girma da Seminar Al-Hafiz Umar Ahmad Mika'il.

Suna farin cikin gaiyatan yan'uwa musulmai zuwa waje Bude Musabaka na Jiha ta Bana 1438/2017, Jigo na 21.

Wadda za'a gabatar kamar haka:

Ranar budewa: Lahadi 30/04/2017

Ranar Rufewa: Laraba 3/05/2017

Lokaci: Karfe 10:00am na safe a kowace rana

Wuri: Babban Masallacin Juma'a na cikin garin Wase, Kofar mai martaba Sarkin Wase.

Manyan baki sun hada da:

1. Babban bako na musamman - Mai Girma Gomnan Jihar Pilato Rt. Hon. Simon Bako Lalong 

2. Shugaban Taro - Mai Martaba Sarkin Kanam Alh. Muhammad Muazu Muhammad II

3. Iyayen Taro - Shugaban Majalisar Malamai na kasa Fhadilatu Ash-sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir da Mai Martaba Sarkin Wase Alh. Muhammad Sambo Haruna.

4. Bako Mai Jawabi - Komishinan Muhalli da Ma'adanai na Jihar Pilato Hon. Abbas Garba Abdullahi 

5- Babban Mai Nasiha - Mataimakin Shugaban majalisar Malamai na kasa na II kuma Uban Matasa Sheikh Sa'eed Hassan Jingir 

6. Babban Mai masaukin baki - Shugaban karamar hukumar Wase Dr. Ado Garba 

7. Masu masaukin Baki - Shugaban majalisar Malamai na Jihar Pilato Dr. Hassan Abubakar Dikko, Shugaban gudanarwa Alh. Dogara Ishaka Dogara, Shugaban Rundunar Yan Agaji Ustaz Muhammad Rabiu Musa da Jami'in lura da Musabaka Al-Hafiz Umar Ahmad Mika'il.

ALLAH YA BADA IKON HALARTA AMEEN

SANARWA DAGA 

Alh. Zakari H. Ambassador (Sakataren yada Labarai na Jiha).