YADDAH LABARAI KE ISKE WANNAN SHAFI DANGANE DA YADDAH TAFSIRAI KE GUDANA A FADIN DUNIYA NA WANNAN QUNGIYA

Submitted by ahmadmd on Mon, 05/29/2017 - 14:26

YADDAH LABARAI KE ISKE WANNAN SHAFI DANGANE DA YADDAH TAFSIRAI KE GUDANA A FADIN DUNIYA NA WANNAN QUNGIYA

ALLAHU AKBAR FADILATU SHEIK MUHAMMAD SANI YAHAYA JINGIR DA HAFEEZ AMINU YUSUF NUHU SUN BUDE TAFSIRI YAU A LAYIN ZANA

Tafseer 2017

LIVE  FROM  JOS, 1/9/1438 H,    27/5/2017 M, 

TAFSIRIN ALKUR"ANI  MIGIRMA DA MASALLACI  JUMA"AH NA YANTAYA  JOS,

************************************************

Fadilatul Shek Muhammad Sani Yahaya Jingir Shugaban malamai na kasa da kasa  tare da Hafiz Aminu Yusuf Nuhu suna gabatar da tafsirin Alkur"ani maigira Allah yasaka musu da Alheri Ameen

(2)Daga nan babban birnin kano, unguwar tal'udu a lokacin da Sheik Yusuf Sambo Rigachikun yake jagorantar bude tafsirin alqur'ani mai girma na wannan shekarar anan babban masallacin kungiya dake unguwar tal'udu.

 

Malam na gabatar da karatu daga karfe 9:00pm zuwa abunda ya sawwaka akowace rana cikin amincewa da yardar Allah. 

 

Muna addu'a dafatan gudummuwa daga Allah akan wannan muhimmin aiki da maluma suke gabatarwa a kowace shekara a mabanbantan garuruwa da gurare, Allah ya sakawa kowanensu da mafificin alhairi. 

 

Allah ya amfanar da al'umma abubuwan da suke karantar dasu, ya karesu daga zamewa ko fadawa cikin kowane abu daka iya kawo damuwa ko hayaniya tsakanin al'umma. 

 

Taken Tafsirin Malam Na Bana Kamar Yadda Ya Ambata shine "Muhimmancin Haduwar Kan Al'ummar Musulmi.

 

Ana iya sauraremmu kai tsaye akan Izalah Online Radio daga karfe 9:00pm zuwa lokacin rufewa In Sha Allahu. Ana kuma iya sauraremmu daga birnin Kaduna daga 5:30pm a gidan radio nagarta na kowace rana, a gidan radion FRCN na kaduna 5:30am.

 

Zamu kawo maku sauran inda zaku iya saurarammu idan yuwuwar hakan ya taso.

(3)Tafseer Ramadan na sheikh abdallahi Mohammed sani. Tare da Allaramma Alhassan Abdallahi  Atebubu /B/A Ghana jibwis N H Q T S JOS NIGERIA

 

(4)Live Update in Jibwis Dukku Nhq Jos  Masjid No 1 Alhamdulillah yau

 1 Ramadan 1438 

27 May 2017 Bude Tafsirin yamma Wanda Ustaz Mustafah Zakariyya tare da Alrm Abdulkadir Abubakar Chiroma Allah yasaka musu da Alkairi ya musu gudumawa.

(5)LIVE FROM MAIDUGURI 

OPENING CEREMONY TAFSIR 

1 RAMADAN, 1438/2017

 

labarin Cikin Hotuna 

 

Wajen Bukin Bude Tafsir Bana 1438 Anan Masallacin Izalah Dake Gwange a Maiduguri. 

 

Wanda Shugaban Malamai Na Borno Sheikh Muhammad Musa Tareda Hafeez Ilyas Haruna Ali Suke Gabatar wa .

 

Mayan Bakin da Suka Samu Halarta Sun hada da 

His Excellency Alhaji Aliyu Abubakar Jato Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Hon. Alhaji Bello Ayuba Secretary APC na Jihar Borno, Hon, Aliyu Ciroma, Prof Sani Saidu Gombe Nat. Legal adviser na Yan Agaji, Alhaji Baba Ba'abba Shugaban Confer Cleaner na Jihar Borno da Sauran Manyan mutane.

 

 

Sheikh Muhammad Musa Ya Fara Tafsir acikin  Suratul At-Taubah Aya 96

 يَحْلِفُونَ لَكُمْ لِتَرْضَوْا عَنْهُمْ ۖ فَإِنْ تَرْضَوْا عَنْهُمْ فَإِنَ اللَّهَ لَا يَرْضَىٰ عَنِ الْقَوْمِ الْفَاسِقِينَ 

 

Allah Yebada Nasaram

(6)Wakilin Ashkh Muh'd sani yahya agarin Zuru, Shugaban Matasa na Kaduna, tare da Alaramma Nafiu usman Bauchi

(7)ALLAHU AKBAR. SHEKARA KWANA INJI MALAM BAHAUSHE:

...................................................

BAKIN RAI BAKIN FAMA GAMU WAJEN BUDE TAFSIRIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA A MASALACIN MU NA DAYA ANAN GARIN LAFIYA FADAR GWAMNATIN JAHAR NASARAWA:

BARA KAMAR YAU MUNA TARE DA MARIGAYI SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI NA JAHAR NASARAWA USTAZ SHU'AIBU ISMAIL:

INA ROKON ALLAH YA YIWA MALAM RAHAMA TARE DA SAURAN AL'UMMAR MUSULMI DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA:

A YAU MUNA TARE DA SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI NA JAHAR NASARAWA:

USTAZ MUH'D SIRAJO ALHAJI SABO HALIFAN MALAM NA FARKO,

MUNA ROKON ALLAH YA AZURTAMU DA YIN AIKI DA ABINDA MALAM ZAI KARANTAR DAMU AMIN,

=======================

(9)Alhamdulillahi rabbil Alamiin shekara kamar Rana, Yau daya ga watan Ramadan jibwis Nat hqt Jos, kumo branch, muke bude tafsirin Alqur'ani Mai girma, Wanda Sheikh Yakubu Muhammad Jama'are tareda Aramma muhammad balarabe Bojude. Zasu gabatar in sha Allahu. Muna Addu'a Allah yamana jagora.Allahu Akbar. 

 

(10)Kai tsaye daga wajen bude tafsir 1438/2017 a garin Bojude, Gombe state wanda Ustaz Ibrahim Muhammad Geidam tare da Hafiz Adamu Muh'd Mangadu Kumo. 

 

Kuma Ustaz Hassan Ya'aqubu Bojude ma ya samu halarta kuma shima zai tafi tafsir a garin Filiya. 

 

Akwai manyan baki da suka halarta, 

 

Allah Ya saka da alkhairi.

(11)Shekara kwana Yau daya ga watan ramadana Allah ya nufi Dr Habib Dan batta da bude tafsirinsa na bana a tsakiyar birnin Gashu'a Yobe State ga Audio na bikin budewa daga Ibrahimawa Gsh.....

(12)Kai saye daga wurin Tafsirin Alqur'ani mai girma  kenan da yafara gudana yau Assabar daga masallacin muslim foundation dake Anka Road G.R.A Gusau. Dai dagacikin malumanmu NA kasa da kasa Dr. Mohammad Tukur Sani Jangebe  ne ke fassara, Alaramma Hamisu sani Kantin Sauki Gusau ne ke fassara. Allah yasa muna daga cikin wadanda za'a yan'ta a wannan wata na Ramadan.ameen

(13)Live daga wajen Tafsir na wannan shekara  1/09/1438 27/05/2017 anan masallacin mini market under jibwis nat hq jos Talata Mafara inda wakilin sheakh Sani Yahaya jingir Wanda yaturo mana wato Ustaz Umar Hassan Gusau mataimakin shugaban majalisar malaimai NA jahar Zamfara da Alaramma Abubakar Habib Riba suke karantar damu acikin Suratul mursalaat Allah yabamu nasara Ameen.

Alhamdulillah 

(14)Bude tafsir alqur'ani kenan wadda sheikh salihu SULAIMAN ningi ZAI gabatar anan Dutse jihar jigawa 

Baki dasuka halacci wurin

Mai girma galadiman Dutse ALH BASIRU sanusi da mai girma secretary gwamnatin jiha ALH fanini da sauran manyan baki

(15)Live update from masjid number 1 jibwis Nat hqt Jos, kumo branch,  bude tafsirin Alqur'ani Mai girma kenan!!  Anan babban masallachin Jumma'a na daya na chikin garin kumo, Wanda babban malaminmu Dr Hafiz Ibrahim Musa Jt, zai gabatar tareda Alaramma Dahiru Abubakar yabi, muna Addu'a Allah yataimaki Malam, Allah yalakkwanta masa Alheri.

(16)LIVE RAMADAN TAFSIR JIBWIS NHQ JOS JAMA'ARE

 

Alhamdulillah Yanzu Haka Muna cigaba da Sauraren Tafsir daga Bakin Wakilin Shugaban Malamai NA Kasa 

 

USTAZ.MUSA SULAIMAN FAUQAL JABAL

DA HAFIZ.ZUBAIRU ADAM IBRAHIM MAI SHAFI 

 

Muna Adu'ah Allah yabasu Nasara 

(17)ALHAMDULILLAH ALLAH YAKADDARI MALAMIN DA NATIONAL TA TUROMANA YASAMU ISOWA WAKILIN SHEK MUHAMMAD SANI YAHYA JINGIR MALAM MUHAMMAD DABO DAGA PLATEAU STATE KARAMAR HUKUMAN KANAM ACHIKIN GARIN DANGI DON GABATAR DA TABSIRIN ALQUR'ANI MAIGIRMA NA WANNAN WATA MAIALBARKA WADDA YAKE GUDANA AHALINYANZU ABAKIN MASALLACHIN JUMMA'A NA JIBWIS TELLA NATIONAL HERT QUATER JOS MUNAMASA FATAN ALKAIRI SHIDA ALARAMMANSA HAFIZ Hassan Saeed Jauro ALLAH YASHIGEMUSU GABA ALLAH YASA YADDA AKAFARA LAFIYA ALLAH YASA AKAMMALA LAFIYA

(18)TARON BUDE TAFSEER

KUNGIYAR J.I.B.W.I.S NHQ JOS NIG,

reshan karamar hukumar kura ,jahar kano,karkashin jagorancin,shugaban malamai Ustaz Lawan Adam Kura, tana farin cikin sanar da kafatanin Al'umar musulmai zuwa gagarumin taron bude tafseer ,wanda wakilin shugaban majalisar malamai na kasa Fadilatush-sheikh Muhammad Sani Alh Yahya Jingir wato Sheikh Muhammad Sani Yunusa Kura Alkali, zai gabatar mana da wannan tafsirin,kuma taron budewar zai gudana ne kamar haka:

RANA:LITININ 03/09/1438H-29/505/2017.

LOKACI:09:30pm

GURI:masallacin jibwis nhq jos ,na tsohuwar kasuwa kura

(19)LIVE UPDATE FROM KAMBA DANDI LOCAL GOVERNMENT KEBBI STATE.

Tafseer by Shk Dr. Mustapha Bashir Niame Niger Rep. And Alaramma Nuraini Sani Kamba Hafiz at juma,at masjid 1 kamba

(20)Live from Jibwis Nhq Jos.

Kano state sumaila

Alhamdulillah!!! Day two of Ramadan.

Yanzu haka za'afara gabatar da Tafsirin Alqur'ani Maigirma na Watan Ramadan na bana 1438/2017 daga daya daga cikin Wakilan Shugaban Majalisar Malamai na Kasa

M HARUNA ABUBAKAR KUMO GOMBE DA

AlARAMMANSA

M ABUBAKAR SULAIMAN SUMAILA

ANAN CIKIN GARIN SUMAILA MASSALACIN MA'AJI SUMAILA KANO

ANA FARAWA 9:00 ZUWA 10:00 AKAMMALA ALLAH YATAIMAKI MALAN DA ALARAMMAH YAYI MUSU JAGORA-------- JIBWIS SOCIAL MEDIA KANO SUMAILA FROM

(21),TAFSIR DAY 1

JIBWIS NHQ JOS

MADOBI LGC

KANO STATE

ALHAMDULILLAH yanzu haka muna sauraron tafsirin alqur'ani daga bakin USTAZ SA'ID IDRIS babban limamin masallacin juma'a na garin madobi 

dake unguwar yan'barkono,dafatan ALLAH yakara taimakon mallam yakara masa kariya da ilmi mai albarka

Mukuma ALLAH yakara mana fahimta 

Live update ayau 2.Ramadan. 1438/28.5.2017

Wannan shine wakilin shugaban mjlsn malamai na kasa,Ustaz Isa Ubaidullahi Musa anan wurin bukin bude Tafsiri Alkur'ani mai girma anan Jibwis Central mosque Mutumbiyu Gassol LGA 2 Taraba state da aiki da abinda za a  Live update ayau 2.Ramadan. 1438/28.5.2017

Wannan shine wakilin shugaban mjlsn malamai na kasa,Ustaz Isa Ubaidullahi Musa anan wurin bukin bude Tafsiri Alkur'ani mai girma anan Jibwis Central mosque Mutumbiyu Gassol LGA 2 Taraba statekoyardamu

(22)Live from Minna Niger state

Kofar gida Malan lad an

Tafsir by Asheikh nasir Abdulmuhyi National admin chairman of Jibwis nhq jos with Hafiz salihu Muhammad.

(23)Tafsir Ramadan daga baki mall Abubakar Abdulsalam Abdussalami Abubakar Jega Anna gari new bussa 

jahar Niger Borgu 28 /05/2017 biyu ga watan Ramandan 

(24)Live @ kontagora

Bikin bude tafsirin alqur ani maigirma wanda babban malaminmu ustaz abdullai abdurrahaman daga abuja

(25)Tafsees Daga Shugaban Malamai Najihar Kogi State Uztaz Idris Adam Alhausawi Da Hafiz Yahaya Ahmad Gombe Amasallacin Juma a Na 1 A Garin Biri Allah Yataimaka

 

(26)Live update Ramadan. 1438/28.5.2017

Wannan shine wakilin shugaban majalisar malamai na kasa,Ustaz Isa Ubaidullahi Musa anan wurin bukin bude Tafsiri Alkur'ani mai girma anan Jibwis Central mosque Mutumbiyu Gassol LGA 2 Taraba state

(27)KAITSAYE DAGA MASALLACIN JUMU'A NA JIBWIS NHQT JOS RESHEN KARAMAR HUKUMAR DARAZO WAJEN BUDE TAFSIRIN ALQUR'ANI MAI GIRMA WANDA USTAZ ILYASU IBRAHIM MAI GATARI SHUGABAN MALAMAI NA JIHAR JIGAWA YAKE GABATARWA AYAU 2 GA RAMADAN.

(28)ALHAMDULILLAH CIKIN IKON ALLAH YANZU HAKA ANBUDE TAFSIRIN MATA NA JIBWIS NHQ JOS JAMA'ARE TAREDA WAKILIN SHUGABAN MALAMI NA KASA

MAL.MUSA FAUQAL JABAL

DA HAFIZ.ZUBAIRU IBRAHIM MAISHAFI

MUNA ADU'AH ALLAH YABASU GAGARUMAR NASARA DA TEMAKO DAGA ALLAH

(29)Jibwis N H Q Jos Munasauraron Bude Tafsin Alqur ani Agarin Biri Wanda Uztaz Idrir Sarkin Hausawa Shugaban Malamai Najihar Kogi State Kegabatarwa Da Alarammansa Hafis Yahaya Ahmad Gombe Kumaga Sauran Shugabanni Na biri Munafata Allah Yataimaka

(30)JIBWIS NHQ JOS RESHEN JINGIR

Yau asabar 1, ga Ramadan 1438 dai-dai da 27/05/2017. Gamu a gaban Ustaz Shitu Sahran da mai ja masa baki Alaranma Isa Abubakar, a Masallacin Juma'a na cikin garin Jingir domin cigaba da gudanar da tafsirin Alqur'ani mai girma, dafatan Allah ya bada ladan sauraro, amin

(31)Live update from Bauchi Bakin Kura Street Central mosque Izalah Jibwis Nhq Jos

National Tafsir Yau Daya Ga Ramadan 1438

Muna Kara godewa Allah Wanda yakawo mana

Sheikh Muhammad Muhammed Bello Adam Saminaka Tareda Hafiz Yusuf Shuaibu Sambo Luti

Yanzu haka akegabatar da jawabin budewa Ga kuma Manyan baki da na Maluma nacikin garin Bauchi Muna Addu'an Allah Yasa Afara a sa a Ameen

(32)LIVE FROM JOS SOUTH RAMADAN TAFSIR A YAU 28/05/2017 AKABUDE TAFSIRIN AL'ANI MAI GIRMA A MASALLACIN JUMMA AH NA YANLILO CIKIN GARIN BUKUR JOS TAKUDU WANDA AKE GABATARWA NA DARE DAGA BAKIN SHUGABAN MALAMAI NA KANAM USTAZ ABUBAKAR YADUDU TAREDA ALARAMMA ZURQARNAINI ALLAH YA SAKA MUSU DA ALJANNAH

 

(33)LIVE UPDATED FROM BIU.

RAMADAN TAFSIR OPENING CEREMONY.

PHOTO NEWS.

A yau Allah ya kaddari akayi bukin bude tafsiri na Alqurani mai qirma da aka saba gabatarwa a Ramadana a Jibwis central masjid opp Gssss Biu.

Mai gabatarwa shine : shaik Ibrahim Muhammad Gunda da alaramma Suleiman Musa Abdullah.

(34)Live update RAMADAN TAFSEER daga talata mafara local government, zamfara state jibwis nhq Jos Wanda mataimakin shugaban majalisar malammai na jahar zamfara na daya MALAM UMAR HASSAN GUSAU tareda Alaramma ABUBAKAR HABIB RIBAH.

Alhamdulillah TAFSEER yayi tafseer fatan mu Allah ya bamu ikon aiki da abunda muka saurara 

(35)Tawagar Alhafeez Aliyu Abdulwahab Jos Amasarautar Deba.

Alhamdulillah Allah ya kaddari Wakilin Shugaban majalisar Malamai na kasa da kasa Alhafeez Aliyu Abdulwahab Mataimakin Shugaban Malamai na jihar plateau.

Wadda yazo garin Deba Don gabatar da tafsirin Alkur'ani Maigirma Na watan Ramadan.

Wadda ya kai ziyara a masarautar Deba don Gabatarda Ta'aziyya Dakuma ziyara kamar yadda kowani shekara ake gabatarwa A fada Allah ya bashi nasara 

akana abinda yazo yi.

(36)IZALA ABIRNIN ZAZZAU AYAU NE AKABUDE TAFSIRIN RAMADAN ABIRNJN ZAZZAU INDA WAKILIN MALAM SHEIK KHALID YAKUB HUSAINI PROVOSTE NA N.C. FATISKUM KEMANA TAFSIR A SURATUL ALI IMRANA DAGA AYA NA DAYA ZUWA NA UKU TARE DA ALARAMMA USMAN SAIDU WARSHU.

(37)ALHAMDULILLAH A YAU 28/05/2017 2GA RAMADAN ALLAH YA KADDARI BUDE TAFSIRIN AL QUR'ANI MAI GIRMA WANDA AKASABA A MASALLACIN JUMMA AH NA YANLILO BUKUR JOS TAKUDU WANDA BABBAN LIMAMIM MASALLACIN YABUDI WATO USTAZ AHAMAD USMAN MUHAMMAD TAREDA ALARAMMA MUSA ABUBAKAR KHALID ALLAH YABADA NASARA

(38)ALHAMDULILLAH

LIVE UPDATE FROM BAWA JANGWARZO JUMUAT MOSQUE

SABON BIRNI LOCAL GOVT

INDA MUKE SAURARON BUDE TAFSIRIN ALQURANI MAI GIRMA DAGA BAKIN SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI NA KEBBE LOCAL GOVT

SOKOTO STATE

SHEIKH HAMISU SHUAIBU UNGUSHI TARE DA ALARAMMA MUKHTARI DAN MALAM

(39)Live From Maiduguri

1 Ramadan Tafsir 1438/2017

Wanda Maitaimakin Sakataren Malamai Na Kasa Sheikh Modu Mustapha Maiduguri Yake Gabatarwa da Harshen Kanuri

Anan Masallacin Imam Bukhari Dake Moduganari bye pass, Maiduguri.

Sheikh Yafara Tafsir Acikin Suratul Baqara aya ta 190

ﻭَﻗَﺎﺗِﻠُﻮﺍ ﻓِﻲ ﺳَﺒِﻴﻞِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻳُﻘَﺎﺗِﻠُﻮﻧَﻜُﻢْ ﻭَﻟَﺎ ﺗَﻌْﺘَﺪُﻭﺍ ۚ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻟَﺎ ﻳُﺤِﺐُّ ﺍﻟْﻤُﻌْﺘَﺪِﻳﻦَ

(40)Alhamdu Lillah ayanzu haka anbude Tafsirin Alkur.ani mai girma a masallacin Juma.a dake Kwa.kwa uku Agege jahar Lagos wanda ya bude shine Ustaz Muhammad Bara.u Kodineto na jahar Lagos kuma Babban Limamin Masallacin tare da Shugaban Alarammomi kuma shugaban Matasa na jahar Lagos anfa rane kafin mai gurin yazo wanda aka turo a mataki na kasa ina rokon Allah yabamu nasara

(41)KEFFI RAMADAN TAFSIR 2017! KEFFI RAMADAN TAFSIR 2017!!

KEFFI RAMADAN TAFSIR 2017!!!

*Jawabin bude Tafsirin Al-Qur'ani Mai Girma na Watan Ramadan*

Daga Bakin: USTAZ ABUBAKAR SALIHU ZARIA (HafizahulLah)

RANA: ASABAR 27/05/2017

Wuri: MASALLACIN JUMA'AH NA BIYU NA SABON LAYI KEFFI, JAHAR NASARAWA.

Lokaci: Bayan sallar Isha'i

Allah Ya bada ikon Halarta. Amin

(42)Daga Sheik Isa Ali Pantami

Idan Allah Ya kai mu Ramadan lafiya, za mu gabatar da Tafsir a Masallacin Juma'a na Annur da ke Wuse 2, Abuja.

Tafsir na Maza: da Yamma daga 5pm-6pm in sha Allah, kowace rana.

Tafsir na Mata: Asabar da Lahadi 11am-12noon na rana.

Mai gabatarwa: Isa Ali Ibrahim Pantami.

TAFSEER din zai kasance da harshen Turanci da Hausa, in sha Allah.

A sanar da masu bukatar zuwa ko da ta hanyar sharing announcement, please.

Allah Ya kai mu ga Ramadan cikin lafiya da imani,... HAKA MUKAI TA SAMUN ROHOTONNIN BUDE TAFSIRAI A FADIN KASA NAJERIYA DAMA KASASHEN WAJE WANNAN SHI YAKE NUNA AIKIN ALLAH SAI MAI YI DON ALLAH.ALLAH YASA A KAMMALA LAFIYA SUKUMA 'YAN UWAH 'YAN INTERNET COMMITTEE DA SUKAI TA YADA WANNAN SAKO ALLAH YASAKA MASU DA ALKHAIRI BAKI DAYA YASA MUNA MASU RABO DA WANNAN WATAN MAI TATTARE DA TARIN ALBARKA AMEEN NAKU DAN UWAH MODDIBBO KATAGUM