IZALAH TA ZIYARCI SOJAN NAJERIA A MAIMALARI

Submitted by ahmadmd on Sat, 06/10/2017 - 15:17

.IZALAH TA ZIYARCI SOJAN NAJERIYA......

Qungiyar Jama'atul Izalatil Bidi'ah Wa'Ikamatus Sunnah Mai National Hedikwatar a Jos, Reshen Jihar Borno. 

Karkashin Jagorancin Shugaban Malamai Na Jihar Borno Sheikh Muhammad Musa Sun Ziyarci Sabon Shugaban Rundunar SOJAN Najeriya Na 7 Division a Maiduguri.

*Sheikh #Muhammad #Musa Bayan Ya Yabawa Sojojin irin kokarinda Sukeyi Wajen Ya Kar da Yan Ta'adda, kuma Yayi Musu Nasiha Kamar Yadda Addini Ya Tsara , Akarshe Sheikh Ya Gabatar Musu Kadan Daga Cikin Tarihin Qungiyar da Manufar Kafuwar sa kuma Yabasu Shawarwari Da Dama.

*Shi kuma Sheikh #Modu #Mustapha -Sakataren Malamai Na Kasa , Bayan Shi Ma Ya Yaba musu irin kokarin da Sukeyi, kuma Yayi musu Nasiha Ya Basu Sharawa Akan Cewa Kada Su Raina Yan kasada su Wajen Daukar Shawara Allah Idan Yaga Dama Zaibaiwa Wani Kurtun SOJA Batsira da Hangen Nesa Wanda Shi Shugaba Bashi da Shi.

*Da Yake Mayar da Jawabi Shi GOC Na 7 Division #Brig Gen. Ibrahim Yusuf Yace Gaskiya Yayi Matukar Farin Ciki da Wannan Ziyarar da Aka Kawo Mishi, Kuma Ya Yabawa Qungiyar Izalah Irin Karantarwan da Sukeyi Wajen Wayar da Kan Al-Umma da Muhinmancin Zaman Lafiya da Tarbiyan da Sukeyi.

Akarshe Yabada Shawara ga Qungiyar Suci Gabada Wa'azozin Sa a Masalataiya, Anguwanni, Gidan Radio da Sauran Wurare Musamman Akan Muhimmancin Zaman Lafiya da Kuma Su Wayar da Kan Al-Umma kan illar ta'adanci da Sauran Abubuwa.

Akarshe Shugaban Malamai Na Jihar Borno Sheikh Muhammad Musa Shi Yarufe da Adu'a.

Kadan Daga Cikin Tawagar Mallam Sun Hada da 

Sheikh Modu Mustapha Maiduguri Asst National Sec C/Ulama'a of JIBWIS, Ustaz Engr. Baba Bello National #Auditor General of JIBWIS, Ustaz Engr. Muhammad Zannah #Admin Chairman JIBWIS Borno State 

da Sauransu.

Allah Yebada Ladan Wannan Ziyarar

13th Ramadan, 1438

8th June, 2017