WAJIBI NE GA DUK WANDA YA YI SALLAR IDI RANAR JUMA'A - YA HALARCI SALLAR JUMA'A

Submitted by adamkabir on Tue, 08/29/2017 - 17:50
WAJIBI NE GA DUK WANDA YA YI SALLAR IDI RANAR JUMA'A - YA HALARCI SALLAR JUMA'A!!!!! Lura da ganin cewa, Sallar Idin Layya ta 1438 ta fado ranar Juma'a, wasu Malamai sun fara fatawowi cewa "IDAN IDI TA FADO RANAR JUMA'A, AN DAUKE MUKU JUMA'A". Lallai wannan fatawa ba dai dai ba ne kuma muna Kira ga masu irin fatawowin nan su ji tsoron Allah, domin Allah zai kama su da batar da mutane ba tare da hujjoji ba. Malam Mai Fiqhul Maliki wa Adillatuh, ya kawo BABI musamman akan Haduwar Idi da Juma'a, sai ya kawo bayanin kamar haka: إجتماع عيد و جمعة. روى إبن و مطرف وإبن الماجشون عن مالك جواز أن يأذن الإمام فى التخلف عن الجمعة إذا اجتمع عيد و جمعة، و ذلك لما يلحق الناس من المشقة: والدليل: الإجماع: وذلك أن عثمان قد أذن لأهل العوالي فى ذلك. و فى الحديث: عن إبن عباس أن رسول الله صلى الله عليه وسلم خرج يوم الفطر فصلى ركعتين لم يصل قبلها و لا بعدها - متفق عليه. Babi akan Haduwar Idi da Juma'a rana daya; Ibn Wahab, da Madraf da Ibn Majishun duka sun ruwaito daga Maliku yi wu wan Jagora ya yi wa mutane izini akan dauke musu sallar Juma'a idan ta hadu da idi. Kuma wannan izini ana yi ne saboda sauqaqa wa mutanen wahala akan dawowa su gabatar da Sallar Juma'a bayan sun yi sallar idi. Dalilin wannan rangwame kuwa an samo shi ne daga Amirul Mumineena Usman bin Affan R.A. Lallai Usman bin Affan ya yi wa Sababbin shiga musulunci a zamanin sa uzurin cewa Lallai idan suka halarci Sallar idi, to ba sai sun sa ke shan wahalan fitowa daga kauyukan su kuma domin halartan Sallar Juma'a ba. Kuma akwai Hadisin da wasu su ke dogara wannan Hujja a kan sa, Wato Hadisin da Abdullahi Dan Abbas R.A ya ke cewa: ANNABI SAW YA FITO YA GABATAR DA SALLAR IDI RAKA'A BIYU KUMA BAI YI WATA SALLAH KAFIN SALLAR IDIN BA, HAKA NAN KUMA BAI YI WATA SALLAR BAYAN IDIN BA. Bukhari da Muslim duka sun ruwaito Hadisin a babin Sallar idi. To yanda Haqiqanin al'amarin ya ke, shi ne: و روى إبن القاسم عن مالك أن ذلك غير جائز، و أن الجمعة يلزمهم، و أن المكلف مخاطب بهما جميعا، العيد على أنه سنة، و الجمعة على أنها فرض. Haka nan kuma Abdulrahman bin Kasim ya ruwaito daga Imamu Maliku yana cewa; Lallai hakan ba dai dai ba ne saboda Juma'a ta kama su, domin abu ne da aka umurci dukkan Wanda Shari'a ta hau kan sa ya gabatar da su gabadaya. Sallar Idi Sunnah ce, ita kuwa Sallar Juma'a Farilla ce. والدليل على ذلك: 1- قوله تعالى: ((إذا نودي لصلوات من يوم الجمعة فأسعو إلى ذكر الله)) وجه الدليل: أنه تعالى يخص عيدا من غيره فيجب أن يحمل الأمر على عمومه إلا ما خصه الدليل. Dalili na farko akan Wajibcin Halartan sallar Juma'a bayan an dawo daga idi (idan lokacin juma'an ya yi) fadin Allah SWT inda Yake cewa: YA KU WADANDA SUKA YI IMAMI, IDAN AN KIRA SALLAR JUMA'A, TO KU YI GAUGAWA DOMIN HALARTAN INDA AKE AMBATON ALLAH (Wato ki halarci Sallar Juma'a). Wannan ayar dalili ne saboda Allah Bai kebance wasu mutane akan su halarci Sallar idi ba, saboda haka ana daukan Gamammen umurni ne sai dai in an samu Dalilin da ya kebanta. 2- أن الفرائض ليس للأئمة الإذن فى تركها، و إنما ذلك بحسب العذر، فمتى اسقطها العذر سقطت، و لم يكن للامام المطالبة بها....... Hujja ta biyu ita ce: Lallai duk abun da yake Farilla ne ba bu wani Jagora da yake da ikon ya bayar da Izinin ayi ko a bari, A'a akan yi haka ne Kawai idan an samu wani uzuri da ya lazintar da yin hakan, Amma a duk lokacin da uzurin ya kau, to kuma Babu wani dalili na yin hakan...... 3- أن الصلاة العيد سنة، والجمعة فرض و لا يسقط الأضعف الأقوى. Hujja ta uku ita ce, Ita Sallar Idi Sunnah ce, ita kuwa Juma'a Farilla ce saboda haka babu yanda za a yi Sunnah ta dauke Farilla. Da wadannan kwararan hujjoji nagartattu Imamu Maliku ya kafa hujja akan cewa: DUK WANDA YA YI SALLAR IDI, TO JUMA'A TANA NAN A MATSAYIN TA TA WAJIBI A GARE SHI. Daga Ustaz Muhammad Nasiruddeen Ibrahim In ba Lalacewa da rudar da Jama'a ba, In Ameerul Mumineena Usman bin Affan ya yi Ijtihadin sa saboda Nisa da wahalan tafiya daga kauyukan Madina zuwa garin Madina saboda hadurran da ke hanya da sauran su - a matsayin Uzuri, Kai kuma yanzu wane irin Wahala ne zai hana ka halartan masallacin Juma'a a cikin gar