KADAN DAGA JAWABIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI NASABUWAR SHEKARA.

Submitted by ahmadmd on Tue, 01/02/2018 - 08:11

Kanun Jawaban Shugaba Buhari Na Sabuwar Shekarar Miladiya.

Cikin wannan safiya na bi sahun yan uwana yan Najeriya domin marhabun da sabuwar shekarar 2018. Alkawuran cikin wannan shekara zasu kasance masu matukar muhimmanci a tafiyar Chanji.

Nayi matukar takaici da na fahimci cewar bukukuwan Kirsimeti da subawar shekarar bana babu komi cikinta face sakonnin gaisuwa, maimakon muyi amfani da bukukuwan wajen nuna kauna da kyautatawa junan mu, wasun mu sun zabi su kirkiri wahalar man fetur duk domin su kawo wahala a cikin kasa.

Sakamakon haka dayawa ba zasu iya yin bulaguro ba sannan kadan da zasu iya yi kuma sai sun yi bulaguro mai tattare da tsada. Wannan abune wanda ba zamu yadda dashi ba, shiyasa muka umurci hukumar NNPC ta dau matakan da suka dace domin ganin man fetur ya wadata. Ina shaida muku cewar zamu magance faruwar haka nan gaba.

Ire iren wadannan rashin kishin kasa, ba zasu kauda gwamnatin mu daga turbar da muka dauru akai ba. Wajibi ne mu sauya dabi'u domin samun cigaba ko kuma a barmu a baya.

Jawabin da zan yi a wannan safiya ya ta'allaka ne akan shaida muku irin kokarin da gwamnati keyi domin dakile tarun matsalolin kasarnan.

Gina manyan tituna da fadada su, aikin layin dogo da samarda tashoshin wutar lantarki a cikin kasa.

* TITUNAN JIRGIN KASA

A bangaren gina hanyar jirgin kasa na zamani, ana cigaba da aikin layin dogo na zamani daga Lagos zuwa Kano.

Kafun shekarar 2019 ta kare aikin zai isa har zuwa Ibadan, idan an kammala shi zai ke diban Fasinjoji Miliyon Biyu ko wace shekara, sannan jiragen daukar kaya zasu ke dakon ton miliyon Biyar a a shekara. Hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasa.

Cikin wannan shekara za a fara aikin layin dogo daga Kano zuwa Kaduna wanda muke kyautata zaton kammala shi a shekarar 2019. Kafun karshen shekarar 2021 layin dogo zai hada cibiyoyin kasuwancin Kudanci da Arewaci.

Layin dogon Abuja zuwa Kaduna zai ke jigilar fasinjoji ma'aikata masu zuwa Abuja su dawo kullum miliyon daya a kowace shekara sakamakon karin kayan aiki da zai samu ranar Alhamis mai zuwa.

Zamu farfado da zurga zurgar jiragen kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri, wanda ya hada da Aba, Owerri, Umuahia, Enugu, Awka, Abakaliki, Makurdi, Lafia, Jos, Bauchi, Gombe, Yola da Damaturu. Layin dogo daga Abuja zuwa Itakpe zai bi ta Baro sannan ya karkare a Warri inda zamu gina sabon tashar jiragen Ruwa.

Muna kokarin cimma yarjejeniyar aikin gina sababbin layin dogo daga Kano zuwa Maradi na jamhuriyar Nijar wanda zai wuce ta garuruwan Kazaure, Daura, Katsina, Jibia, zuwa Maradi.

* MANYAN TITUNA

Manyan tituna 25 zasu amfana da shirin SUKUK na Naira Biliyon 200. Ko wanne sashi na kasarnan zai samu Biliyon 16.67. Daga cikin wadanda zaa fi maida hankali sune

a. Oyo – Ogbomosho,

b. Ofusu – Ore – Ajebandele – Shagamu,

c. Yenagoa Road Junction – Kolo Otuoke – Bayelsa Palm,

d. Enugu – Port Harcourt Dual Carriage Way,

e. Onitsha – Enugu Expressway,

f. Kaduna Eastern Bypass,

g. Tagwayen titunan Kano – Maiduguri,

h. Tagwayen titunanAbuja – Lokoja – Benin,

i. Tagwayen titunan Suleja – Minna.

Zaa fara ikin sabunta titin Abuja – Kaduna – Zaria – Kano kuma zaa kammala kafun shekarar 2019.

* WUTAR LANTARKI

Shugaba Buhari ya bada tabbacin kyautatuwar wutar lantarki cikin wannan shekara inda ya zayyano wasu tashoshin wutar lantarkin da gwamnati take ginawa.

- Tashar wutar lantarkin Katsina zata samarda 10 Megawat kuma zai fara aiki cikin wannan shekara.

- Tashar wutar lantarkin Zungeru 700 Megawat zaa kammala shi a shekarar 2019.

- Tashar wutar lantarkin Gurara 30 Megawat, Kashimbilla 40 Megawat da kuma Kaduna 215 Megawat, zasu kammala cikin wannan sabuwar shekara.

- Tashar wutar Mambilla wanda yayi shekaru 40 ba a kula dashi ba, Zamu kammala shi a shekarar 2023.

Shugaba Buhari ya godewa yan Najeriya bisa yadda sukayi ma shi addu'oi a lokacin da yake karbar magani a birnin Landan.