WAKILAN AL KHAIRI DAGA JOS ZUWA MAIDUGURI

Submitted by ahmadmd on Fri, 01/12/2018 - 09:26

Labari Cikin Hotuna 

 

Wakilai Ta Musamman Daga National Hedikwatar JIBWIS Sun Ziyarci Sheikh Modu Mustapha Maiduguri ...

 

Wakilan Shugaban Majalisar Malamai JIBWIS Na Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahaya JINGIR Sunkawo Ziyara Ta Musamman Wajen Sheikh Modu Mustapha Maiduguri anan Gidan Sa Dake Cikin Birnin Maiduguri, Jihar Borno. 

 

Sheikh Col Adamu Girbo Muhammad Rtd, Sheikh Aliyu Bara, Ustaz Dauda Kaloma Suka Wakilci Shugaban Malamai Na Kasa. 

 

Bayan Sun Isar da Sakon Sheikh JINGIR kuma Sunyi Mishi Adu'a Ta Musamma Akan Allah Yekara Mishi Lafiya Kuma Jinyar da Yayi Yesa Kaffara Ce Agareshi.

 

Shugaban Malamai Na Jihar Borno Sheikh Muhammad Musa Shi Ma Ya Nuna Farin Cikinsa da Godiyar sa da Wannan Ziyarar ta Musamman. 

 

Nashi Jawabi Sheikh Modu Mustapha Yayi Farin Ciki da Wannan Ziyaran Na Yan Uwan TakaTa Addini kuma Ya Nuna Matukar Godiyar Sa Ga Shugaban Majalisar Malamai Na Kasa Yadda Yake Numa Mishi Soyayya, Kuma Yayi Adu'a Ta Musamman Kamar Yadda Addini Ya Hadamu Yesa Mu Dauwama Acikin sa Kuma Yahada Fuskokin Acikin Jannatul Firdous.

 

Sheikh Modu Mustapha Maiduguri Shine Mataimakin Sakataren Malamai JIBWIS Na Kasa, Wanda Yayi Fama da Jinya a Kwanakin Baya  Wanda Yanxu Alhamdulillah Yasamu Lafiya. 

 

Allah Yebada Ladan Wannan Ziyara kuma Yahada Kan Malamai Mu Akan Gaskiya, Yebamu Lafiya da Zaman Lafiya 

 

Baba Mala Meleh 

Director Borno State 

JIBWIS Social Media 

11 Jan, 2018