KO KAYARDA KO BAKA YARDABA !!!!!!! KO KANA SO KO BAKASO

Submitted by ahmadmd on Fri, 03/02/2018 - 23:48
SHEIKH ISMA'ILA IDRIS YA GINA ALKHAIRI YANA BIYE DASHI CIKIN KABARINSA HAR ZUWA ALJANNAH. Sheikh Isma'ila Idris ya kafa alkhairi kuma ya gina alkhairi a rayuwarsa kafin mutuwa. An wayi gari duk mutumin kirki yau a Nigeria na fatar a kirashi dan IZALAH ahlissunnah. Duk Malamin Izalah idan ya hau Mimbarin Izalah yace Bismillah, Sheikh Isma'ila nada kamasho a cikin ladarsa. Ballantana Makarantun Islamiyyoyi dake cikin Kasar nan. Har wayau Malam nada kamasho a cikin Hudubobin Limamai da Alarammomi Mahaddata Alqur'ani. Yana da kamasho cikin 'yan Kasuwa ahlissunnah da Ma' aikata dake tafiyar da al'amurransu akan ilmi. Sheikh Isma'ila Idris na samun kamasho daga kyakkyawar aiki da 'yan dariku da sauransu sukayi koyi da Izalah kamar : Kafa Islamiyya, sanya Hijab, koyi da wa'azin Kasa dana Jiha da Kananan Hukumomi, duk basu sansu ba farko, sun koya ne daga Kungiyar Alkhairi ta Izalah. Sheikh Isma'ila Idris bin Zakariyya Malamin Malaman zamaninsa ne, ko sun kiya bale sun yarda. AllaH Ya jikan Malam Ya gafarta masa.