HADIN KAN AL-UMMAR MUSULMAI FARILLAHNE BA......….

Submitted by ahmadmd on Wed, 03/07/2018 - 14:29

Sambo Rigachukun Sheikh Yusuf 

To muna fatan Allah ya kara hada kammu akan gaskiya Domin ni dai dan gajeren zangon ilimina abinda yake sanar dani shine duk lokacinda kaga al,ummar musulmi cikin kaskanci da wulakanci To sun bar Allah ne ,Amma idan har musulmi suka bar Allah sukayi watsi da bin Sunnar manzon Allah suka koma basu da banbanci dasu da wadanda ba musulmiba wajan aikata kowani irin nau,in sabon Allah To wallahi su saurari zuwan Bal,i Ayoyi da dimbin hadisai duk sun tabbatar da haka To kuma Ni babban abinda yafi damuna shine malamai sun kasa yarda su hada kai waje daya kuma wallahi badan komai bane , sai don Son Duniya na neman shugabanci da son daukaka .Anyi watsi da abinda hadisi da tauhidi suka tabbatar mana na cewa kowa Allah ya riga ya rubuta mishi nau,in irin arzikinshi da abinda zai samu da abinda zai zama tun yana cikin cikin mahaifiyarshi 1 an rubuta arzikinshi 2 an rubuta ajalinshi 3dama irin nau,in aikinshi 4 haka kuma an riga an rubuta Shi dan wutane ko dan aljanna ne To idanko har da gaske mun fahimci haka to Menene abin fada ko rikici ko jayayya 

Kuma su malamai sunefa likitocin Duniya akan ko wace irin cuta da zata kama dan Adam To sai suma suka kamu da irin wannan cutar To yaya zasu iya gyara wani? Mutum ne yazo maka da maganin Mura yana Talla To amma kuma shima gashi yanata Atishawa kuma ruwan majinar mura yana zubowa daga hancinshi To yaya zaayi kasayi maganin tunda shima mai sayar da maganin bai warke ba 

Saboda haka Malamai kuji tsoron Allah ku hada kai domin kawunan mabiya ya hadu guri daya 

Domin duk matsalar daga wajenkune da zarar kun gyaru to Suma mabiya zasu gyaru wanda kuma yaki To mu sai mubar ai,amarinshi zuwa ga Allah shi Allah shi yasan abinda zai iyayi da bawanshi in yaso yana iya shiryar dashi ya ganar dashi ko kuma yayi mishi Talala kullun yayita zaton ai shi akan dai dai yake har ya mutu ya koma ga Allah Allah ya kamashi a madakata  Kuma Wallahi idan da Zaka kasa su mabiya dake dukkan bangarorin 95/ bisa 100 wallahi basason rabuwar domin baabinda suke amfana da ita sai cusa musu kiyayyar juna da gaba da aibanta malamansu na Sunnah da suke amfana dasu Saboda haka yan kadan ne daga cikin manyan malaman Su suke amfana da rabuwar Domin sun toshe wata kafa da Arzuki ke bubbuga masu ta dalilin Kungiyar Abindama Suka mallaka wallahi ita kantama kungiyar bata dashi Kuma idan kayi magana sai mabiyansu suce ai Su wane Manyan yan kasuwane Kuma sai ka rasa irin nau,in kasuwancin da sukeyi  Domin yanzu da zarar kace Aliyu Dan gote Dan kasuwane To kowa zai yarda da kai domin yasan irin nau ukkan kayan kasuwancinsa da kuma dinbin yawan kamfanoninsa da irin abinda yake shigowa dashi a kasa da dimbin yaransa masu sarrafa dukiyarsa da dimbin barorinsa da kuma masu amfana dashi To Alhamdu lillahi Allah dai yasa mai rabo ya gane Domin kai mabiyi Ya kamata ka fahimci idan alqiyamata ta tsayu dangantakarka da wani ba zata amfanekaba matukar kana binshi akan son zuciya 2 Kuma na biyu ina jan hankalinka kada ka yarda kai ka bata taka Lahirar dan Duniyar wani  3Da soyayya da kiyayya matsakaici akeyi Maana ,shine karka zurfafa soyayyar masoyi  

Idan kayi haka sai ka kasa gano kuskuren masoyi saboda ka makance 

Kuma karka zurfafa kiyayyar wanda kake Qi Shima idan ka zama haka sai ka kasa yi mishi adalci a lokacin da ya fadi gaskiya ko a inda yayi dai dai Allah yasa mu dace