SHEKARARTA ARBA'IN YAU

Submitted by ahmadmd on Mon, 03/12/2018 - 16:23

IZALA TA CIKA 40 Da sunan Allah mai rahama mai Jin kai. Muna godiya gareshi muna neman tsarinsa da sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Duk wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi Wanda ya batar babu mai shiryar da shi. Muna godiya ga Allah da ya nuna mana wannan rana da kungiyar JAMA,ATU IZALATUL BID,AH YAU TA CIKA SHEKARA ARBA,IN. KO BA KOMAI LALLAI AN SHA GAGARUMAR JARRABAWA WACCE TAKE CIKE DA AYYUKAN DA A LOKACI GUDA BAZA A TABA LISSAFA SU BA. AMMA DOLE DUK MANAZARCI YAYI LA,AKARI DA DAUKI BA DADI DA WANDA ALLAH YASA WANNAN KUNGIYAR TA KAFU KARKASHINSA. WANNAN KUWA BA KOWA BANE ILLA ASH SHEIKH ISMA,ILA IDRIS IBN ZAKARIYA JOS. AN HAIFI MALAM A WANI GARI DA AKE KIRA GOSKOROM A GUNDUMAR ZUNGUR A KARAMAR HUKUMAR BAUCHI. MALLAM BAFILLACE NE GABA DA BAYA. YAYI KARATU A WURIN MAHAIFIYARSA DA MAHAIFINSA KAFIN YA FITO WAJE CIKIN GARIN BAUCHI NEMAN ILMI. MALLAM YAYI KARATU A WURIN MALLAM YAKUBU MAIDAJIN KO MALLAM NA KAN KUSURWA DA BABBAN LIMAMIN BAUCHI NA LOKACIN MALLAM IMAM MAHMUD KAFIN MALLAM YA JE KADUNA NEMAN ILMI A WURIN BABBAN ALKALI KUMA MALAMIN TAUHIDI ASH SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMMI. MALAMI YAYI KARANTARWA A MAKARANTU DA YAWA KAMA DAGA GARIN TULU CIKIN KARAMAR HUKUMAR TORO HAR YA ZUWA CIKIN GARIN KADUNA. Mu kwana nan zamu dora da ikon Allah