HADINKAN AHALIN SUNNAH ALKHAIRINE WALLAHI

Submitted by ahmadmd on Mon, 03/19/2018 - 10:02

Ahlussunnah naci gaba da hada kawunan su a inuwa daya Dan isar da sakon Allah a borno.

 

Kamar yanda kwanakin baya na fada muku a, ci gaba da hada kawunan Ahlussunnah a jihar borno yana samun nasara Sosa, kwamitin Sheikh Abba'aj Islamic Foundation dake kar kashin Sheikh Ibrahim Mustapha, ya sake shirya wa'azi a jiya inda ya hada malamai daga bangarori biyu baki daya wato izalar Jos da Kaduna Kamar yanda ake kiran su a inuwa daya Dan isar da sakon Allah (swt).

 

Kamar yanda jagoran taron ya fada, "Rumfar dake bayana duk wani malami da aka sanshi a borno yana nan zaune anan, walau daga Kaduna ne ko jos, ya kara da cewa, " Muna fadan Kaduna ko jos ne badan banbanci ba Dan haka aka saba kira, malamin yace mun samu nasarar hada irin wannan lacca ko MUHADARA sau hudu, kuma duk ban garorin biyu sun bada hadin kai. Alhamdulillah.

 

Malamin da ya gabatar da muhadarar shine,

SHEIKH BARR AHMAD ABDULKADIR, Inda ya gabatar da takarda mai taken matasa Ku KAMA SANA'A.

 

Wadanda sukayi ta'aliki sune ,

SHEIKH BAGONI MUSTAPHA BAMA,

DA SHEIKH MODU MUSTAPHA.

 

Manyan malamai da dama ne suka samu halarta kadan daga ciki sune,

Dr MUHAMMAD ALH ABUBAKAR ,

SHEIKH MUHAMMAD MUSA,

SHEIKH GAMBO KYARI, 

SHEIKH KABIRU GARBA DANYAYA. DS

 

Ana cikin tsaka da muhadara sai ga Dr Abdullahi Usman Gadan kaya, Wanda ya zo wajen, Dama shi yazo Maiduguri ne bisa gaiyatar makarantar Imam malik dake nan Maiduguri, sai malaman sun gaiyace shi da ya halarta kuma yazo yayi magana mun amfana dashi sosai. 

 

Har yake cewa, "ya yaba da wannan taron kuma yayi mamaki kwarai da yanda yaga Ahlussunnah suka hadu haka, kuma malaman suke fadin gaskiya ba tare da shakka ba. Sai yayi addu'a ga al'ummar borno dama Nigeria baki daya.

 

Yaka mata sauran jihohin Nigeria suyi koyi da jihar borno wajen haduwa a inuwa daya dan isar da sakon Allah ba tare da la'akari da wani ban gare ba.

 

Insha Allah idan tafiya tayi tafiya a haka ba'a samu wasu tsofaffi munafukai masu cewa, " Damu aka kafata ba, sai mun canja wannan taken KADUN/JOS.

 

MUHAMMAD ISMAIL ALI