INGANTACCEN TARIHIN IZALAH YAFITO

Submitted by ahmadmd on Wed, 04/04/2018 - 09:20

IDAN RANA TA FITO TAFIN HANNU BAYA KARE TA.

----------------------------------------------------------------

Hakika ba haushe yayi gaskiya, wannan littafi da Ash-Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya rubuta mai suna (TARIHIN JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA'IQAMATIS SUNNAH, A MADUBIN GASKIYA) Nat. Hqtrs, Jos. Aka kuma qaddamar dashi ranar lahadi 2/4/2018M A Babban birnin tarayya Abuja, Akwai fa'idodi masu tarin yawa acikin sa.

Wannan littafin ba tarihin Izala kawai ya kunsa ba, ya kunshi tarihin kafuwar Musulunci a Nijeriya, da kuma irin illolin da turawan yamma suka yiwa musulunci da musulmai.

Tabbas, ya dace ace kowanne matashin da yake cikin wannan kungiyar ya mallaki wannan littafin, saboda akwai abubuwa masu mahimmaci acikin sa.

Bayan haka, wannan littafin akwai bukatar a yada shi ya shiga ko'ina acikin kasar nan dama wajenta.

Sa'annan akwai bukatar a juya shi zuwa harshen turanci domin wadanda basa jin hausa suma su samu fa'idar da take cikin sa.

Tabbas, Malam yayi gagarimin aiki wajen rubuta wannan littafi.

Wannan gagarimin aiki da Malam ya gabatar muna rokon Allah ya karba masa, ya kara masa Imani da daukaka.

Allah ya taimaki shi shida mataimakansa tun daga mataki na kasa har zuwa rassa.

Allah ya gafarta wa Ash-Sheikh Isma'il Idris bin Zakariyya, da Malamin sa na Tauhidi Ash-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.

Wannan kungiya ta Izalah Allah ya kara mata taimako da dacewa acikin ayyukan da take gabatarwa.

Mai ciwon hassada ne kawai bazai gane mahimmancin wannan littafin ba.

Wannan littafi wata hanya ce da zata kara wayarwa da matasa Kai su kara sanin kungiyar Izalah da kuma irin wahalhalun da aka sha kafin kungiyar ta kafu.

A Kullum gaskiya kara bayyana take yi.

Ga tarihin Izalah Malam ya rubuta, to tunda kuma kunce sunan Kungiyar ku ( JAMA'ATU IZALATIL BID'AH WA'IQAMATIS SUNNAH) Sai Ku rubuta tarihin taku kungiyar mu gani.

ALLAH YA TABBATAR DA DIGADIGAN MU AKAN WANNAN ADDINI NA MUSULUNCI YA KARE MU DAGA BIN SON ZUCIYA.