SHEICK YAYI WA'AZI MAI ZAFI

Submitted by ahmadmd on Mon, 04/16/2018 - 17:02
SHEIKH SANI YAHYA JINGIR YAYI MARTANI GA WAKAR:- Afuwan-Afuwan Ya Barhama::- Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS na Kasa,Mai Head/Qrt's ajos. Ash-sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir Yagabatarda Gagarumin Wa'azi amasallacin Yan-taya agarin Jos aranan Juma'a data Gabata 13-4-2018, Dattijun Shehun Malamin Yayi Doguwar Shimfida Mai Shiga jiki akan abunda Yashafi kadaita Allah agurin bauta,Yakaranto ayoyin Al-qur'ani da hadisan Manzan Allah(S.A.W)Dasuke nuni kan kadaituwar Allah Kuma Suke nunin Cewar Allah shi kadaine,Kuma Kowa da Komai bayinsa ne. Shugaban Malaman na Kasa,Yakara dacewar komai da kowa Allahne Yahaliccesu, Saboda haka duk wanda yace akwai wani abunda Za'a bautatawa bayan Allah,to,kafiri ne. Dayajuyo Ga batun Wakar Kafirci da Wasu Yan-Dariku Sukayi:- Shehun Malamin Yayi Allah Wadare da Wannan Mugun Kafirci nasu data fito fili,Kuma acewar Shehun Malamin Wannan Akidatasu dawasu suka baiyanata,itace Abunda yake cikin littattafansu kuma shine Yahaifarda Tarikar dama,amma Wai Mutum dasunan Musulunci Yazagi Allah,Yace ibrahim kaulaha Yafi Allah,to,ibrahim kaulahadai Yamutu,Allah kuma shine Allah baya Mutuwa,domin mutuwarma Allahne yahalicceta. Dayajuyo bangaren Shugabanni,Malamin Yakirayesu da babban Murya dacewar, "INA KIRAN SHUGABANNI DASUNAN ALLAH KUDAINA BARIN WASU SUNA ZAGIN ALLAH ANAJERIYA,IBRAHIM KAULAHA(INYASI)BA ALLAH BANE,TUNTUNI YAMUTU" Kuma Malamin Yaja hankalin Dukkan Musulmi dacewar Kada Suje Susakaka kansu a irin Wadannan kazamun Akidu ta Zagin Allah. Shehun Malamin Yarufe Jawabansa da Yin Addu'ar fatar al-khairi da Jin-jinawa Ga Sarkin Makkah da Shugaban Kasar najeriya Alhaji Muhammadu Buhari, Allah katsare Najeriya,Allah Yashiryemu,Allah Yatsaremu daga Akidunnan Marasa kyau,Allah Kada ka kamamu kan laifin Wasu lalatattun Cikinmu,Allah Kataimakemu duniya da lahira,Lallai Allah kai mai ikone akan hakan.