JAWABIN SHEICK NA BANA A GARIN ABUJA

Submitted by ahmadmd on Mon, 04/16/2018 - 17:10

ALLAH YA BIYA DA GIDAN ALJANNAH

JAWABIN SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI TA KASA DA KASA

TA HADADDIYAR KUNGIYAR JIBWIS

NATIONAL HEADQUARTERS JOS

ASH-SHEIKH MUHAMMAD SANI YAHAYA JINGIR

WANDA YAYI A RANAR

BABBAN TARO NA SHEKARA-SHEKARA NA KASA

(JIBWIS ANNUAL ISLAMIC CONVENTION ABUJA 1439/2018)

A EAGLE SQUARE DAKE BABBAN BIRNIN

TARAYYAR NIGERIA, F.C.T. ABUJA

A RANAR LAHADI 15 GA RAJAB 1439 DAIDAI DA 1 GA AFRILU, 2018

ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ

ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺑﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﺎﺗﻢ ﺍﻟﻨﺒﻴﻴﻦ ﻭﺇﻣﺎﻡ ﺍﻟﻤﺮﺳﻠﻴﻦ، ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﻣﻦ ﺗﺒﻌﻬﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺪﻳﻦ، ﻭﺑﻌﺪ :

ﺍﻟﺴﻼﻡ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻭﺭﺣﻤﺔ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﻌﺎﻟﻰ ﻭﺑﺮﻛﺎﺗﻪ :

1. Gabatarwa:

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin Sarki mai kowa mai komai, mai rahma mai jin kai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bisu da kyautatawa har zuwa ranar sakamako, Allah yasa da mu cikinsu, amin.

Bayan haka, wannan hadaddiyar kungiya ta JIBWIS wacce marigayi Ash-Sheikh Isma'ila Idris Allah ya kaddareshi da kafawa kamar shekaru talatin da tara da suka wuce, tana wa'azin Musulunci a Nijeriya da kasashen dake makwabtaka da ita a nahiyar Africa da sasannin Duniya akan dukkan fannonin rayuwar Musulmi bisa shari’ar Allah da sunnonin Manzon Allah (S.A.W).

Wannan kungiya tana fifita karantar da tauhidi a matsayin tushen ibada a musulunci, ta hanyar tsarkake Allah (SWT) da kadaita shi a wajen bauta da barin dukkan nau'o'in shirka, Bidi’o’i, bokanci, camfe-camfe, tsafi, da kashe mutane ta hanyar amfani da kungiyoyin asiri, da sauran abubuwa da shari'ar musulunci ta bayyana na haramci.

Har yanzu kungiyar tana wa'azi da karantarwa akan muhimmancin zaman lafiya, da'a ga shugabanni, tausayawa talakawa ta hanyar rike amanar shugabanci da raya ilimi da ilmantarwa don muhimmancisa ga cigaban rayuwar al'umma.

Wadannan ayyuka na wa'azozi da ilmantarwa ana gudanar da su ne ta hanyoyin wa’azin kasa a cikin kasa da waje duk bayan mako uku, wa'azozin jihohi, kananan hukumomi da na rassa, tarukan karawa juna ilimi (Seminar), Gasar karatun Al-Qur'ani mai girma tun daga matakan kasa zuwa rassa, bude makarantu na yara, da manya maza da mata a matakai daban-daban, da tafsirin Al-Qur'ani mai girma a Nijeriya da kasashen waje, bude sashin ilmantar da Alkalai, Shugabanni, Limamai da Ladanai makamar ayyukansu daki-daki da buga littattafai da sauran hanyoyin da suka dace na yada ilimi da ilmantarwa, bayannan da zasu biyo da nasarorin da wannan kungiya ta samu zasu kara tabbatar da manufofinta da ayyukanta, da fatan Allah ya kara mana taimako akan wadannan ayyuka na alheri da ciyar da kasarmu gaba da sauran kasashe, Amin.

2. NASARORI:

Sakamakon ayyukan kungiya da suka gabata da hanyoyin da ake aiwatar da su, kungiyar ta sami nasarori kamar haka:

a) Kungiyar na samun nasarori masu dinbin yawa da karin hadin kai da son juna tun daga kafata har zuwa hadewar wannan kungiyar da Allah (SWT) ya nufeta tayi Ranar 26 Muharram 1433 dai-dai da 21st December 2011. Kungiyar ta samu nasarorin ilmantar da al’ummar Musulmi da makwaftansu wajen kawar da:-

- Jahilci,

- Shirka,

- Bidi’o’i,

- Ki-ki juna na kabilanci da sauran laifuka.

Kuma wannan hadewa ta cimma babbar nasara na haduwar dukkan Ahlus-sunnah muna aiki babu wani ce-ce kuce.

A nan nake kara yabawa mataimakana na daya da na biyu Sheikh Yusuf Muhammad Sambo Rigachukum da Sheikh Sa’id Hassan Jingir da Shugaban Gudanarwa da mataimakansa Sheikh Abdun-Nasir Abdulmuhyi, Alh. Hashimu mai Atamfa Kaduna da Dr. Sani Aliyu Sagir Sokoto da Shugaban Yan Agaji da mataimakinsa Alh. Isa Waziri Muhammad Gombe da Alh. Ibrahim Shu’aibu Ishaq da dukkan shugabanni a matakin Kasa, Jihohi, Kananan Hukumomi, Rassa da sauran ma’aikata da daidaikummu, Allah ya ka ra muku albarka, Ya sa ka muku da alheri.

b) Mun sa mi nasarar gabatar da wa'azozi a mataki na kasa cikin Nijeriya har (10). 1438/2017.

c) Mun yi nasarar tura malaman tafsiri a watan Ramadan wurare daban-daban a cikin kasa da kasashe makwabta har maluma (512) a bana kamar haka:

A: Nijeriya = 369

B: Niger Republic = 61

C: Ghana = 35

D: Burkina Faso = 12

E: Togo = 15

F: Mali = 5

G: Cameroon = 3

H: Sudan = 1

I: Chad = 4

J: Benin Republic = 6

K: Central Africa = 1

Jumla = 512

A matakin jihohi da kananan hukumominsu kuma maluman da suka gabatar da tafsiri maluma 5,673.

d) YAWAN MAKARANTUNMU DA DALIBAN DA KE KARATU A KASA A BANA 1437 –8/2017

i. Yawan Makarantunmu na Malja'us Sunnah

a) Guda = 4784

b) Dalibai = 4,729,186

ii. Yawan Makarantunmu na Asasul Islam

a) Guda = 405

b) Dalibai = 1,930,130

iii. Yawan makarantunmu na Asabar da Lahadi sashen yara

a) Guda = 210

b) Dalibai = 15,340

iv. Yawan makarantunmu na Asabar da Lahadi sashen manya

a) Guda = 230

b) Dalibai = 16,006

v. Yawan Makarantunmu na Mu'assasah Tahfizul Qur'an

a) Guda = 364

b) Dalibai = 197,500

vi. Yawan Makarantunmu na Secondary

a) Guda = 65

b) Dalibai = 135,250

vii. Yawan Makarantunmu na Higher Islamic Studies

a) Guda = 75

b) Dalibai = 90, 005

viii. Yawan Makarantunmu na sashen Diploma, NCE wanda mukayi nasarar bude su a Jos National Headquarters, Bauchi, Potiskum, Gombe, Kebbi, Jama'are, Lafia, Keffi, Gumau da Kebbi.

a) Guda = 10

b) Dalibai = 11, 330

xi. Makarantunmu ta horrar da alkalan musabakar Al-Qur'ani, Limamai, ladanai, da shugabannin malamai, gudanarwa da agaji guda daya a hedkwatar wannan kungiya ta kasa Jos mai yawan dalibai guda 180.

JIMLAR MAKARANTUNMU DA DALIBANMU

A BANA 1438-9/2017 - 2018

a) Makarantu = 6,144

b) Dalibai = 7,124,927

e) Mun yi nasarar gudanar da gasar karatun Al-

Qur'ani mai girma jiko na Ashirin da Daya (21) a cikin garin Yola Jihar Adamawa, a mataki na Kasa inda yan takara (108) daga jihohi (19) suka sami shiga wannan gasa.

f) Munyi nasarar gudanar da taron karawa juna sani na (24) a matakin Kasa (Semina) inda Jihohi (31) da kuma makobtanmu Niger Rep. da Benin suka sami halarta. Inda wadannan Jihohi suka turo mutane (1,003) don wannan aiki.

g) Mun yi nasarar kafa cibiyar zakka da wakafi tun daga rassa har zuwa kasa baki daya. Wannan cibiya an kafata ne don wa'azi akan muhimmancin zakka, karbo zakka a hannun mawadata, rabata ga wadanda shari'ar musulunci ta ambata da tsoratarwa kan hadarin rashin fidda ita a musulunci. An sami dacewa mai yawa akan wannan aiki da taimakon Allah. A wannan shekara mun sami.

a) Kudi = 5,960,000:00

b) Hatsi buhu = 285

wadanda muka rabasu rukuni-rukuni kamar haka:

* Mabukata

* Ma'aikata

* Gidajen marayu

* Majalisar sa'I

* Makafi

* Kutare

* Tallafi ga dalibai (Scholarship)

* Kwamitin Matasa

* Makarantu

* Asibiti

* Marasa Lafiya

h) Mun yi nasarar kafa kwamitin wa'azin matasa don wa'azantar da su da dora su akan hanya ta kwarai tun daga kasa har zuwa rassa. Kuma sun shirya muhadarori da ziyarce-ziyarce da taimakowa marasa galihu, wanda suka kashe kudi bana har N 2,600,500:00

i) Mun yi nasarar kafa kwamitin sulhu a matakin kasa, jihohi, kananan hukumomi da rassa don warware matsaloli na mu'amala tsakanin musulmai ta hanyar rage zuwa kotuna don kararraki da neman hakkoki.

j) Mun yi nasarar tura rundunar yan agaji sansanin alhazai da filayen jiragen sama daban-daban don taimakawa alhazai a yayin tafiya aikin hajji da kuma dawowarsu wanda yawansu yakai (1,526). Inda ta kasha N 22,425,970:00

k) Munyi nasarar yiwa ma'aikatan wannan kungiya da co'odinetoci bita ta musamman dan sanin makamar ayyukansu.

l) Munyi nasarar bude hamshakiyar Sakatariyar wannan Kungiya, a Hedkwatar ta dake Jos bayan ingantata da fadadata da muka yi don samun saukun aiki, Alhamdulillahi rabbil Alamin.

m) Munyi nasarar rubuta littafi mai suna TARIHIN JIBWIS A MADUBIN GASKIYA wanda na kaddamar a yau wanda Allah ya bani damar rubutawa don fito da tarihin kafuwar wannan kungiya na tsawon shekara arba'in, domin ranar da Sheikh Isma'ila Idris ya kaddamar da ita a Jos na halarci wurin.

BUKATUNMU NA BANA

A bana cikin yardar Allah muna da burin samun N350, 000,000:00 don gina dakin taro, dakin bincike, kayayyakin Ofis da Motocin aiki.

Muna fata jama'a zasu taimaka fisabilillahi don mu cimma burin mu na kammala wannan aiki.

GODIYA DA YABAWA TA MUSAMMAN

* Ina kara godiya ga Allah (SWT) da yake bamu damar gudanar da wannan aiki na yada addinin musulunci.

* Muna godiya ta musamman ga dukkan jagororinmu na mulki na siyasa wadanda suka amsa gayyatarmu don tallafawa raya ilimi da ilmantarwa duk da dinbin ayyukan da ke gabansu, Allah ya saka musu da alheri.

Kuma ina godiya ga dukkan shugabannin wannan kungiya, na majalisar malamai, gudanarwa da yan agaji da dai-daikunmu da wadanda suke taimakawa na musamman a ko'ina suke, bisa tsayuwa akan wannan aikin na ciyar da musulunci gaba Allah Ya saka musu da alheri, amin.

KWAMITOCIN TAFSIR

Muna godiya ga kwamitocin tafsirai na jihohi da kananan hukumomi da rassa akan aikin da suka gudanar a bana aka samu gagarumar nasara, Allah Ya yi kyakkyawar sakayya.

YAN JARIDU

Muna yabawa yan jaridu wajen bada sahihan labarai na gaskiya don cigaban wannan kasa ta mu Nigeria musamman radiyon FRCN Kaduna, jaridar Gaskiya tafi Kwabo, NTA, Africa TV 3, Afrikiy TV, Daily Trust, Radio France International, Voice of Nigeria, Dewtche Welle Radio, BBC world Service, News Agency of Nigeria, The Sun Newspaper, Jaridar Rariya, Leadership/Hausa Newspaper, People's Daily, New Nigeria Newspaper, Crest Newspaper, Voice of America, F.M Radio 90.5, Radio Hamada, Izala Radio, masu Internet din mu, da sauransu, Allah Ya saka musu da alheri.

GODIYA DA YABAWA TA MUSAMMAN

Muna godiya ga Allah (SWT) da yake kara dawo mana da nutsuwa da zaman lafiya a wannan Kasa. Alhamdulillahi Rabbil Alameen.

Muna yabawa wasu gwamnatocin jihohi da mawadata dake bawa dalibai 'ya'yan talakawa tallafin karatu a jami'oi'da wasu manyan makarantu a kasannan.

Muna yabawa dalibanmu wadanda suka kammala karatunsu a makarantu da jami'oi' daban-daban, kuma suke bada gudummawa da bawa makarantunsu kayan aiki da kyautatawa malamansu.

KIRA NA MUSAMMAN

i) Muna kira ga Gwamnatin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da a dawo da hankali kan kara fardado da noma kiwo don mu samu ciyar da kasar mu da makobtanmu sa'annan musama wa jama'ar kasa aikin yi a fagagen nomar da kiwo, da kananan masana'antu.

ii) Gwamnati ta samawa matasa aikin yi a matakai daban-daban ta hanyar farfado da masana'antu manya da kanana da sauransu.

iii) Jagorori da Allah Ya ba su mulki da su tsaya da kyau akan aiyuka bisa gaskiya da amana.

iv) Hukumomi da sauran al'ummar Kasa su kara hattara da hadarin 'Yan Shi'a, 'Yan Boko Haram da dukkan sauran masu ta'addanci da masu yiwa Gwamnati zagon Kasa daga ma'aikatanta.

v) Kira na musamman ga Yan Majalisun Kasa su gyara dokokin zabe

Hukumar zabe ta tsaya sosai wajen tsara ingantaccen zabe da aiwatar da shi cikin tsoron Allah da adalci, kuma muna goyon bayan amfani da na'urar tantance masu zabe (Card Reader) don kawar da magudin zabe.

Dukkan wanda aka zaba a matsayin shugaban Kasa ko gwamnan Jaha ko shugaban karamar hukuma, idan larurar rasuwa ko kasarar da ta kai ba zai iya ci gaba da aikinsa ba lallai a sake zabe a gurbinsa, kada a ce mataimakinsa yah au mukaminsa, domin tabbatar da tsaron shugabannin a fagen rayuwa da lafiyarsu, da baiwa kowane dan Kasa yancin zaben wanda yake so a kan mukamai da yake so da dorewar zaman lafiyar Nigeria da ci gabanta.

Kundin tsarin mulki ya yi bayani da zai warware cikas na tsarin fadar Shugaban Kasa da yan Majalisan dokoki da na Dattijai irin abubuwa masu hana Kasa ci gaba sakamakon takaddama.

KIRA GA TALAKAWA:

1. A Kula da ilmi na addini da na sana'a

2. Ayi Biyayyar da ta dace don Allah, ga shuwagabanni

3. Kuma ayi Aiki tukuru don nema da kuma cin halal

4. A Kula da hadin kai akan gaskiya da zaman lafiya

5. Sa'annan a kasance da Wadatuwar zuci, kuma duka don Allah babu kyashi babu hassada.

KAMMALAWA

A karshe muna mika godiyar mu ta musamman ga dukkan jama'a mahalarta da jami'an tsaro da dukkan jami'an Gwamnati wadanda suke taimakawa wajen tsaro da kare kasa cikin taimakon Allah.

Haka kuma muna yiwa kasarmu addu'a ta fatan alkhairi da zaman lafiya. Allah ya bamu ikon aiwatar da dukkan abubuwan da aka ambata, cikin gaskiya da rikon amana.

Muna yiwa Shugaban Kasarmu na Nigeria Alh. Muhammadu Buhari addu'ar Allah Ya taimake shi, Ya ba shi nasara, Ya kara bashi kariya daga dukkan sharrin makiya da azzalumai, Ya ba shi mashawarta na gari da za su taimake shi cikin wannan aiki.

Muna ka ra addu'ar Allah (SWT) Ya jikan Mu'assisin wannan kungiya Ash-Sheikh Isma'ila Idris da Malaminsa na Tauhidi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Allah Ya jikansu, Ya raya zuriyarsu ya jikan dukkan wadan da suka rigamu gidan gaskiya cikin wannan aiki har zuwa ranar tashin kiyama. Allah Ya sakawa kowa da alkhairi kuma ya mayar da kowa gidan sa lafiya kamar yadda muka zo lafiya.

Ina yiwa mataimakana wajen wannan aiki addu'ar Allah ya kara musu albarka ya saka musu da alkhairi, su ne Sheikh Yusuf Sambo Rigachukum da Sheikh Sa'id Hassan Jingir Sheikh Abdun-Nasir Abdul Muhyi, Alhaji Isa Waziri Muhammad Gombe da mataimakansu (Wuzara'u Sidikin) da dukkan jagorori na kasa da na jihohi da kananan hukumomi da rassa da dai-dai kunmu, Allah ya sakawa kowa da alheri.

Muna kuma kara maimata yabo da godiya ga Allah (SWT) da salati ga Manzon Shi Annabi Muhammad (S.A.W) kamar yadda muka bude wannan jawabi.

Wassalamu Alaikum Warahmatullahi Ta'ala Wabarakatuh

NAKU

Sauban Y. Khalid

JIBWIS Jos North

Internet Media

Committe.

Saubanykhalid4real@gmail.com.