TSOHON MALAMI A MAKARANTAR SARKIN MANGU YA ZAMA LIMAMIN SULTAN BELLO

Submitted by ahmadmd on Thu, 01/05/2017 - 13:39

An haifi Dr. Suleiman a ranar 14 ga
watan Yuni, shekara ta 1962.
Imam, Dr. Suleiman Muhammad Adam
ya samu shaidar karatu ta PhD guda
biyu a karatun Fiqhu sannan ya mallaki
shaidar karatu ta Masters Degree a
fannin ilimin addinin musulunci da
harshen Larabci.
Harwayau kuma ya mallaki shaidar
karatu ta, Bachelor of Arts (LLB), yana
kuma da Degree a fannin Sharia.
Yayi karatunsa a kasashen Madina,
Saudi Arabia, Malaysia da Nigeria.
Sannan ya halarci kwasa-kwasai da
taruka da dama kuma ya gabatar da
kasidu a ciki da wajen kasarnan.
A yanzu haka dai shine babban malami
a sashin koyar da ilimin addinin
musulunci na jami'ar jihar Kaduna.
(KASU)Malami a Jami'ar Jihar Kaduna ya
zama babban limamin masallacin
Sultan Bello
Idan dai ba'a manta ba rikicin limanci
ya barke a masallacin tun bayan da
Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta nada
babban sakatarenta, Dr Khalid
Abubakar Aliyu limancin masallacin.
Wasu daga cikin jiga-jigan masallacin
karkashin fitaccen Malamin nan, Dakta
Ahmad Gumi suka ki amincewa da
nadin akayi bore lamarin da ya munana
har takai ga Gwamnan jihar Kaduna,
Malam Nasir Elrufai ya shiga tsakani.
A watan Oktoban 2016 Gwamnan ya
gayyaci masu ruwa da tsaki na
masallacin, ciki har da mai martaba
Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris,
Sheikh Dr Ahmad Gumi, Dr. Khalid Aliyu
da wakilan JNI da na kwamitin
masallacin Sultan Bello da kuma
wakilan hukumomin tsaro suka gana a
gidan Gwamnati Jihar Kaduna da nufin
warware takaddamar da ta tashi akan
limancin.
Bayan tattaunawa da jin korafin kowane
sashi sai El-Rufai ya bukaci Dr. Khalid
ya sauka a nada wani limami saboda
maslaha.
Daga nan sai Gwamnan ya bukaci a
nada kwamiti da zai jagoranci fitar da
limami, a inda Gwamnan ya bukaci
masarautar Zazzau ta kawo wakilai 6,
JNI, Kwamitin masallaci, makarantar
Sheikh Gumi duk su kawo mutane Uku-
Uku.
A inda anan take aka kafa kwamiti kuma
aka basu sati Biyu su gabatar da
rahoto.
A bangaren masarautar Zazzau, Alhaji
Shehu Idris ya mika, Alhaji Ibrahim
Muhammad Aminu (Wazirin Zazzau),
Dalhat Kasimu Imam (Shugaban
Limaman Masarautar Zazzau),
Mohammed Sani Yakubu (shugaban
JIBWIS na Zaria), Aminu Dantsoho
Abdullahi (Shamakin Zazzau), Dr. Bello
Abdulkadir (Salanken Zazzau)
da kuma Balarabe Sa'idu Yahaya
(Mukaddas).
Bangaren Dakta Gumi kuma suka tura
Sheikh Ahmad Gumi, Brigediya Janar
AbdulQdir Gumi da Mallam Tukur Mamu
(Dan-Iyan Fika).
Sai bangaren Jama'atu Nasril Islam
suka tura Umar Ahmed Zaria, Yusuf
Ahmad Bida da Yusuf Sa'idu
Mohammed. A yayinda kwamitin
masallaci suka tura tsohon sakataren
Gwamnati, Balarabe Idris Jigo, Kaptin
Mohammed Joji da Alhaji Jibrin
Mohammed.
Kwamitin ya fara zamansa na farko
domin nemo mafita a ranar Laraba 9 ga
watan Nuwamba.
Majiya ta shaida mana cewa bayan an
kai ruwa rana a tsakanin kwamitin
game da hanyoyi da ka'idojin da
matakan da za a bi wajen fitar da liman
din sai aka cimma matsaya.
Shugaban kwamitin Wazirin Zazzau sai
ya bukaci duka bangarorin su fitar da
wakili dai-dai da zasuyi alkalancin
jarabawar da za'a yiwa yan takarar
limancin masallacin.
Bangaren Sheikh Gumi sun gabatar da
yan takarar su kamar haka: Dr.
Suleiman Muhammad Adam, Alaranma
Usman Muhammad, Ustaz Hussein
Zakariya Yawale, Imam Usman
Abubakar, Mallam Umar Osamat Idris
da kuma Mallam Sa'idu Abubakar.
Sai bangaren JNI suka gabatar da
Dr. Lawal Sule Abdullahi, Mallam
Muhammad Rabiu Zakariyau,
Dr. Abdulmalik Ahmad Jafar da Mallam
Sa'idu Abubakar Muhammad a
matsayin yan takaransu.
A yayinda Mallam Aminu Abdullahi
Yusuf, Mallam Aminu Yusuf Abdullahi,
Mallam Abubakar Sani Hussain da
Mallam Aliyu Al-Hafiz Muhammad suka
mika sunayensu a matsayin yan takara
masu zaman kansu kowanensu na
neman limancin masallacin.
A karshe dai Gwamnan ta hannun
Shugaban hukumar kula da sha'anin
addini, Engr. Namadi M. Musa ya fitar
da zakara a cikin yan takarar su 13
bayan shirya masu jarabawar gwajin
fahimta ('Interview') domin gane hazaka
da gogewarsu da zurfin karatunsu da
cancantarsu.
Majiya ta tabbatar da cewa tun a watan
Nuwamba 2016 kwamitin ya gabatar da
rahotonsa kamar yadda aka bukaceshi.
Bayan kammala yiwa yan takarar
jarabawa gwajin fahimta ne sai dan
takaran da Sheikh Ahmad Gumi ya
gabatar wato Dr. Suleiman Muhammad
Adam ya lashe jarabawar da maki 80%.
Kuma a ranar 4/01/2017 aka aikewa da
Sheikh Dr. Suleiman din takardar
nadinsa limancin Sultan Bello daga JNI
ta hannun mai martaba Alhaji Shehu
Idris daga ofishin sarkin musulmi mai
alfarma Sa'ad Abubakar.
Sanarwar ta ce a yau Alhamis
5/01/2017, Dr. Suleiman zai sha nadi
daga mai martaba sarkin Zazzau a
fadarsa domin shirya limancin sallar
Juma'a a gobe 6/01/2017.
Wani dan jarida Sani Baba Ahmad ya
ruwaito adadin kason da kowannensu
ya samu a jarabawar gwajin fahimtar
kamar haka :-
Aliyu Al-Hafiz ya samu maki 52%,
Dr. Lawal Abdullahi 78.7%,
Abubakar Sani 78.7%,
Dr. Ahmad Jafar 74.7%,
Umar Osamat 55.3%,
Aminu Abdullahi Yusuf 54.7%,
Mohammed Zakariyau 48%,
Aminu Yusuf Abdullahi 62.7%,
Usman Ahmed 68%,
Sa'idu Abubakar 60%,
Dr Suleiman Muhammad Adam 80%
Sannan sai Hussain Zakariya Yawale ya
lashe maki 60%.Allah yabash ikon jagorancin jama'a akan Gaskiya