JAWABIN SHEICK SANI YAHYA JINGIR A TARON KASA A GARIN ABUJA

Submitted by ahmadmd on Thu, 03/30/2017 - 22:57
JAWABIN SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI TA KASA TA HADADDIYAR KUNGIYAR JIBWIS NATIONAL HEADQUARTERS JOS, ASH-SHEIKH MUHAMMAD SANI YAHYA JINGIR A RANAR BABBAN TARON NA SHEKARA SHEKARA NA KASA WANDA AKA GUDANAR A EAGLE SQUARE DAKE BABBAN BIRNIN TARAYYA, ABUJA A RANAR LAHADI 1.GABATARWA:- Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga ALLAH madaukakin sarki mai kowa mai Komai ,mai rahama mai jin kai tsira da amincin ALLAH ya tabbata ga shugabanmu Annabi MUHAMMAD S A W da iyalansa da Sahabbansa da wandada suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako. ALLAH ya sa da mu cikinsu. Amin. Bayan haka, wannan hadaddiyar kungiyar ta JIBWIS wacce marigayi ASH-SHEIKH ISMAILA IDRIS ALLAH ya masa rahama ya kaddare shi da kafawa kamar shekaru talatin da tara da suka wuce, tana WA'AZIN musulunci a Nijeriya da kasashen makwafta da ita a Nahiyar Afrika da sassan duniya akan fannonin rayuwar musulmi bisa shariar ALLAH da sunnonin Manzon ALLAH S A W. Wannan kungiya tana fifita karantar da tauhidi a matsayin tushen ibada a musulunci ta hanyar tsarkake ALLAH SWT da kadaita shi a wajen bauta da barin dukkan nauoin shirka bidioi bokanci camfe-came tsafi da kashe mutane ta hanyar amfani da kungiyoyin asiri da sauran abubawa da Sharia musulunci ta bayyana na haramci. Har yanzu kungiyar tana WA'AZIN da karantar wa akan muhimmancin zaman lafiya, Da'a ga shugabanni,tausayawa talakawa ta hanyar rike amanar shugabnaci da raya ilimi da ilmantarwa don muhimmancinsa ga cigaban rayuwar al'umma. 2.NASARORI sakamakon ayyukan kungiya da suka gabata da hanyoyin da ake Aiwatar da su, kungiyar ta sami nasarori kamar haka :- a) kungiyar na samun nasasori masu dinbin yawa da karin hadin kai da son juna tun daga kafata har zuwa hadewar wannan kungiyar da ALLAH S W T ya nufeta tayi Ranar 26 muharram 1433 dai dai da 21th December 2011. Kungiyar ta samu nasarorin Ilmantar da AL'ummar MUSULMI da makwaftansu wajen kawar da :- Jahilci Shirka bidi'o'i Ki-ki juna na kabilanci da sauran laifuka. Kuma wata babbar nasara ita ce koyawa jamaa tafiya cikin tsari da hadin kai wanda ya kai ga kawar da sabanin da kungiyar tayi fama da shi na tsawon shekaru 21. Kuma wannan hadewa ta cimma babbar nasara na haduwar dukkan Ahlussunnah muna aiki ba wani ce-ce Luce. A nan nake kara yabawa mataimakana na daya da na biyu sheikh yusuf Muhammad Sambo rigachikum da sheikh saidu Hassan jingir da shugaban gudanarwa da mataimakinsa Ustaz Abdulnasir Abdulmuhwi, Alhaji Hashimu Mai Atamfa Kaduna da Dr. Sani Aliyu Sagir Sokoto da shugaban 'yan agaji da mataimakinsa Alh. Isah Waziri Muhammad Gombe da Alh. Ibrahim Shuaibu Ishaq da dukkan shugabannin a matakin na kasa da jihohi, kananan hukumomi, da rissa da sauran daidaikunmu ALLAH ya kara muku albarka, ya saka muku da alheri. b) mun samu nasarar tura Malaman tafsir a watan Ramadan wurare daban daban a cikin kasa da kasashen makwafta har maluma (492) a bana kamar haka : A: Nigeria = 354 B: Niger = 58 C: Ghana = 34 D: burkina faso=12 E: Togo. =15 F: Mali = 4 G: Cameron =3 H: Sudan. =1 I : Chad. = 4 J: Benin REP. =6 K: Central Africa =1 A matakin jihohi kananan hukumomi kuma maluman da suka gabatar da tafsiri maluma 5,381 d) YAWAN MAKARANTUNMU DA DALIBAI DAKE KARATU A KASA A BANA 1437-1438/2016-2017 I. Yawan marantunmu na Malia'us sunnah a) GUDA = 4764 b) DALIBAI = 4,696,186 ii. Yawan makarantunmu na asasul islam a. GUDA = 387 b. Dalibai = 1,747,390 iii. Yawan makarantunmu na asabar da lahadi sashen yara a. GUDA 203 b. Dalibai 11,406 iv. Yawan makarantunmu na asabar da lahadi sashen manya a. GUDA = 221 b. Dalibai = 11,406 v. Yawan makarantunmu na mu'assasah Tahfizul Qur'an a. Guda = 344 b. Dalibai = 117,500 vi. Yawan makarantunmu na secondary a. GUDA = 64 b. Dalibai = 129,964 vii. Yawan makarantunmu na Higher Islamic studies a. GUDA = 73 b. Dalibai = 81,084 viii. Yawan makarantunmu na sashen Diploma, NCE wanda mukayi nasarar bude su a jos national headquarters, BAUCHI, Potiskum, Gombe, Kebbi, jama'are, Lafiya, Gumau da kebbi. a. Guda = 10 b. Dalibai = 7,601 Xi. Makarantunmu ta horar da alkalan musabakar AL-Qur'ani, Konami, Dalibai, da shugabannin malamai, gudanarwa da agaji guda daya a headquarters wannan kungiya ta kasa jos mai yawan Dalibai guda 156. JIMILLAR MAKARANTUNMU DA DALIBANMU A BANA a) Makarantu = 6,061 b) Dalibai. = 6,865,077 e) Mun yi nasarar gudanar da gasar karatun AL-Qur'ani mai girma jiko na ashirin (20) a cikin garin jos jihar Plato, a mataki na KASA inda yan takara (109) daga jihohi (18) suka sami shiga wannan gasa. f) Munyi nasarar gudanar da taron karawa juna sani na (23) a matakin kasa (seminar) in jihohi (29) da kuma makobtanmu Niger Republic da Benin suka sami halarta. Inda wannann jihohi suka turo mutane (883) don wannan aiki. g) Mun yi nasarar kafa cibiyar Zakka da wakafi tun daga rassa har zuwa kasa baki daya. Wannan cibiyar an kafata ne don WA'AZI akan muhimmancin Zakka, karbo Zakka a hannun mawadata, rabata ga wannanda shariar musulunci ta bayyana da tsoratarwa kan hadarin rashin fidda ita a musulunci. An sami dacewa mai yawa akan wannan aiki da taimakon ALLAH. A wannan shekara mun sami. a) kudi = 5,880,000:00 b) Hatsi buhu = 283 Wandanda muka rabasu rukuni-rukuni kamar haka : * Mabukata *Ma'aikata *Gidajen marayu *Majalisar sa'i *Makafi *Kutare *Tallafi ga Dalibai scholarship *Kwamitin matasa *Asibiti *Marasa Lafiya h) Mun yi nasarar kafa Kwamitin WA'AZIN matasa don wa'azantar da su da dora su akan hanya ta Kwarai tun daga kasa har zuwa rassa. Kuma sun shirya muhadarori da ziyarce-ziyarce da taimakawa marasa galihu, wanda suka kashe kudi bana har # 2,556,700:00 I) Mun yi nasarar kafa Kwamitin sulhu a matakin kasa, jihohi kananan hukumomi da rassa don warware matsaloli na mu'amala Tsakanin musulmi ta hanyar rage zuwa kotuna don kararraki da neman hakkoki J) Mun yi nasarar kafa tura rundunar yan agaji sansanin alhazai a yayin tafiya aikin hajji da kuma dawowarsu wanda yakai (1,326) . inda ta kashe # 21,425,970:00 K) A bara mun yi burin aiwatar da cigaba da ayyukan da muka fara na ginin masallaci,makar anta da ofisoshi a Guzafe nan ABUJA (JIBWIS ISLAMIC CENTER GUZAFE, ABUJA). Kuma wadannan ayyuka mun yi nasarar gudanar da su da dan abin da ALLAH ya sa muka samu baki dayansu na daidai ruwa daidai gari, ALLAH ya saka da alheri. BUKATUNMU NA BANA A bana cikin yardar ALLAH muna da burin samun naira milyan 175,000,000:00 don karin kayayyakin aiki na kimiyar fasahar bayanai ta yanar gizo, motocin aiki da sauran kayayyakin aiki. Muna fata jama'a za su taimaka fisabilillah don mu cimma burin mu na kammala wannan aiki. Daga Hamza Muhammad Sani, National Organising Secretary Jibwis Internet Committee Nhq Jos