YAUMA KAMAR KULLUM NASIHAR JUMA'A

Submitted by ahmadmd on Sun, 04/02/2017 - 00:07

Yau juma,a 03/07/1438-31/03/2017 kamar kullum gashi sati ya zago,wancan satin munata shirin tafiya wa,azin Abuja,gashi Allah ya kaimu kuma an gabatar har sati yayi muna addua Allah yasanya mana a mizani.Gamu a gaban shugaban majalisar malamai ta kasa Assheikh Muhammad Sani Yahaya jingir yana karantar damu addini kamar yadda yasaba,a karshe malam yayi addua da bangajiya ga al,ummar wannan kungiya da fatan kowa ya koma gida lafiya,wadanda sukayi shahada Allah ya gafarta musu yasa aljannah ce makomarsu,marassa lafiya Allah yabasu lafiya yasa kaffara ne.