SANARWAR DAGA MAKARANTAR ALKALAI DA LIMAMAI LADANAI DAKE GARIN JOS

Submitted by Anonymous (not verified) on Mon, 04/03/2017 - 09:16

Qungiyar jama,atu Izalatil bid,atu wa,iqamatis Sunnah mai headquarter a garin jos, karkashin jagorancin shugaban majalisar malamai ta kasa Assheikh Muhammad Sani Yahaya jingir, Tana sanarda bude makarantar Alkalai da Limamai da Ladanai da Shugabanni da Yan,agaji cewa, inshaa Allahu ranar 10/04/2017 za,a bude Makarantar,kuma za,a fara karatun ne a Wannan Rana ta Litinin.Insha'Allahu Kuma za,a fara register ne tun ranar asabar 08/04/2017 A harabar makarantar Dake Sarkin Mangu jos. Sanarwa daga shugaban makarantar Alkalai, Hafiz Aminu Yusuf Nuhu. Kuma dukkan mabiya susani cewan uwar kungiyah tasa sabuwar doka, Dokar da aka kafa a tsarin wannan tafiya yanzu itace_duk wanda baiyi wannan makaranta ba to bazai zama alkalin musabaka ba. Sanarwa ta fito ta hannun Hamza Muhammad Sani National organising secretary jibwis internet committee Nhq jos.