JAWABIN TA'AZIYYAH DA S M S Y J YAGABATAR

Submitted by ahmadmd on Thu, 04/06/2017 - 11:02

JAWABAN SHEIKH SANI YAHYA JINGIR GAME DA ZAMAN DA SUKAYI DA SHEIKH ALHASSAN SA'ID A RANAR TALATA,....

-

A cikin Jawaban da Sheikh Sani Yahya Jingir ya gabatar a Masallaci Yau da Asubah ya mika ta'aziyyarsa ga Iyalai da kuma Abokan Aiki da sauran Jama'ar musulmi na rasuwar Babban Malami Dr.Alhassan Sa'id Adam Jos.

Cikin Jawaban sai yace: "Munyi zaman mitin na coucil of ulama da Sheikh Ahassan Sa'id ranar talata anan cikin garin Jos, dama Majalisar council of ulama mutum uku ne ke Jagoranci:

1. Sheikh Balarabe Dauda (Shugaba)

2. Sheikh Sani Yahya Jingir (Mataimaki na 1)

3. Sheikh Alhassan Sa'id (Mataimaki na 2).

Bayan rasuwar Sheikh Balarabe sai Majalisa ta zauna ta nada Sheikh Sani Yahya a matsayin Shugaba, Inda Sheikh Alhassan Sa'id ya zama mataimaki na 1, Sheikh Abdurrahman Lawan mataimaki na 2.

Sheikh yaci gaba da cewa, "A cikin zaman da mukayi shekaranjiya talata Sheikh Alhassan Sa'id sai yake cewa, "Nikam kamar nafi kowa jin dadin zaman da mukeyi, Ina bada shawara akan a kara yawan yan Majalisar Council Of Ulama, saboda wasu sun rasu, kamar

Alh. Abubakar Hamma

Alh. Inuwa Turakin Jos

Sheikh Balarabe Dauda. Dss.

Ya kamata mu kara yawan yan Majalisar ba sai kwananmu ya kare ba.

Sai Sheikh Jingir yace masa, to musa ranar da za ayi zama na gaba, sai Dr.Alhassan yace, "AMMA FA BA ZAN SAMU DAMAR ZUWA BA, Domin zanje ganin likitana na kwana goma a kano"

Sai Sheikh yace masa "Allah ya kara lafiya To a cikin Almajiranka akwai M. Aliyu Aliyu sai ka masa bayani a rubuce don ya wakilceka".

Dr. Yace "Ina bada shawarin duk wanda za a dauka kada a dauki wanda zai rika daukar labaranmu yana kaiwa kafirai"

Sheikh Jingir yace, "Gaskiyane wannan,

Mukayi Addua aka tashi daga mitin cikin farin ciki da juna".

Sai Jiya ake sanar dani Rasuwarsa a can kano din.

Allah ya Jikansa, Ya Gafarta masa kura-kuransa, Ya kyautata namu bayansu.

-Jawaban Sheikh Sani Yahya Jingir kenan da yayi akan zaman da sukayi ranar talata a Jos.

-

Rahoto: Sadik Jibrin Daga Birnin Jos.

YSR HRN MHD

(Jibwis Internet Media Commitee).

09/07/1438 AH

06/04/2017CE