YAU MA KAMAR KULLUM NASIHAR JUMA'A DAGA BAKIN SHUGABAN MAJALIASAR MALAMAI NA KASA

Submitted by ahmadmd on Fri, 04/07/2017 - 20:52

Alhamdulillahi yau juma,a 10/07/1438-07/04/2017 muna cikin alhinin na rasuwar Babban malami masanin addini Dr.Alhasan Saeedu Adam muna addua Allah ya jikansa.

Gamu kuma munzo masallaci dan gabatarda sallar juma,a anan yantaya jos,kamar yadda aka saba kafin zuwan liman ga Shugaban majalisar malamai ta kasa nan Assheikh Muhammad Sani Yahaya jingir yana karantar damu addini musamman akan tauhidi da fiqhu.

Malam yajinjina halin da muka samu kammu a kasar nan musamman akan jagoranci yadda shugabannin kasar suke ta rudani,malam yayi addua Allah ya hadama kansu dan su hadu ayi mana aiki.

Malam yayi addua ga shugaban kasa Muhammad Buhari Allah yakara masa lafiya,ya kuma taimakeshi da mataimaka na gaskiya.

Malam yakarayin addua ga marigayi Dr.Alhasan Saeed Adam jiya yaje shida mataimakansa sun gabatar da ta,aziya ga iyalansa,muna addua Allah ya gafarta masa.

Sannan Malam yakara ta,aziya ta rasuwar Malam lawan sakataren ayyuka na Reshen Rafin pa a jos,muna addua Allah ya gafarta masa,mukuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani.