BUDE MAKARANTAR LIMAMAI DA LADANAI DA ALKALAI

Submitted by ahmadmd on Mon, 04/10/2017 - 19:17

LIVE FROM JOS, 13/7/1438 H, 10/4/2017 M,

BUDE MAKARANTAR ALKALAI DA LIMAMAI DA LADANAI DA SHUWAGANNI,

************************************************

Fadilatul shek Muhammad Sani yahaya jingir Shugaban malamai na kasa da kasa yana gabatar da jawabi awajan bude makarantar horar da Alkalai da ladanai,

Shugaban malaman yayi godiya ga Allah da yabawa manzon Allah da yabawa jahohin kungiyar nan bisa kokari wajin bin tsarin na karatu da karantaswa kuma yace ilmi shi yakafa kungiya dan haka dolene asami dan izala ahalussunah akan layi na karatu da sunan Allah ,

Kuma yaja hankalin dalibai da sumai da hankali akan abin da yakawosu sucire lalaci suyi karatu da rubutu bakasala.

Kuma daga karshe yace kada suyi sakaci da riko da tauhidi da sakaci da akida ta sunnah tsantsa daga karshe yagabayar da cewa yabude wannan horar da alkalai da limamai da suna Allah .