ALLAH KA JIKAN ALHAJI AMADU CHACCHANGI

Submitted by ahmadmd on Thu, 04/20/2017 - 09:01

KULLU NAFSIN DHA'IKATUL MAUT!!!

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UUUNN!!!

AllaH (swt) Ya fadi gasikiya. "Duk wata rai dake zaune a doron Kasa zata Qare."

Alhaji Ahmadu Chanchangi, babban mai dukiyar albarka, dukiyar da AllaH (swt) da kanSa Ya tsare Ya tsarkake, mai dukiyar Musulunci, dukiyar Talakawa, yau rayuwarsa tazo karshe.

Idan mutane basu manta ba, sau biyu ina sanar daku halin rashin lafiyar da Alh. Ahmadu Chanchangi ya shiga tare da neman addu'arku, bayan ya samu sauki an sallameshi daga Asibiti ya koma gida, sai rashin lafiyar bayan kwana biyu ta sake dawowa. Na sake neman addu'ar jama'a zuwa gare shi. Daga karshe ashe ciwon abokin tafiya ne.

AllaH Ya gafartawa Alh. Ahmadu Chanchangi, AllaH Ya kyauta Makwancinsa, AllaH Ya lullube shi da jin qanSa da Rahamarsa. AllaH Yasa mutuwarsa ta zama hutawa a gare shi. AllaH Yasa ayyukansa Na alkhairi su bishi har cikin Kabari, su kasance abokan firarsa har zuwa ranar sakamako.

Rasa wannan Gwarzo a fagen fidda hakkin AllaH da basheta zuwa ga talakawa (Zakka) tamkar irin rashin da 'yan arewacin Nigeria suka taba yine na rashin Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello, wanda har gobe ake ambatonsa da alkhairi, kamar haka, Alh. Ahmadu Chanchangi ba za'a maida kamarsa ba a fagen bin umurnin AllaH da fidda Zakka kamar yadda AllaH Yace a fitar kuma ba za'a taba mantawa dashi ba har abada, In Shaa AllaH! .

Alh. Ahmadu Chanchangi ya dade yana karantar da 'yan'uwansa masu dukiya dake zaune a Kano Kaduna Lagos Abuja da sauran sassan Nigeria don su fito suyi koyi da shi wurin bin umurnin AllaH amma sun kau da kai.

AllaH Ya jikan Sheikh Abubakar Mahmud Gummi, wanda shine ya dora wannan bawa nasa akan kyakkyawar hanya na alkhairi.