JIBWIS NHQ JOS

WAJIBI NE GA DUK WANDA YA YI SALLAR IDI RANAR JUMA'A - YA HALARCI SALLAR JUMA'A

Submitted by adamkabir on Tue, 08/29/2017 - 17:50
Lura da ganin cewa, Sallar Idin Layya ta 1438 ta fado ranar Juma'a, wasu Malamai sun fara fatawowi cewa "IDAN IDI TA FADO RANAR JUMA'A, AN DAUKE MUKU JUMA'A". Lallai wannan fatawa ba dai dai ba ne kuma muna Kira ga masu irin fatawowin nan su ji tsoron Allah, domin Allah zai kama su da batar da mutane ba tare da hujjoji ba.